1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon tashin hankali a ƙasar Mali

Usman ShehuSeptember 30, 2013

Dakarun gwamnati da mayaƙan MNLA sun yi arangama a arewacin Mali, abin da ke nuna har yanzu da saura a batun zaman lafiyan ƙasar

https://p.dw.com/p/19rhs
epa03173145 (FILE) A file photograph dated 21 October 2011 shows Tuareg rebel fighters moving through northern Mali on a pick-up truck with a mounted heavy machine gun, near Kidal, Mali. Reports on 06 April 2012 indicate that a Tuareg rebels group known as the National Movement for the Liberation of Azawad (MNLA) in the north of Mali have declared independence for a region they are calling Azawad, after seizing control of the area following their advances southward and in the wake of the 21 March coup. It called on the international community to recognize the new nation and said it would respect the borders of neighbouring states. The UN Security Council on 04 April condemned the rebel attacks in northern Mali and called for an end to the violence. The rebels took the historic city of Timbuktu at the weekend with the help of Islamist groups. EPA/Tanya Bindra
Mayakan Abzinawa na kungiyar MNLA a MaliHoto: picture-alliance/dpa

A ƙasar Mali bayan zaman lafiya da aka samu 'yan watannin da suka gabata, wani sabon tashin hankali ya ɓarke a arewacin ƙasar. Rohotonni suka ce dakarun gwamnati da 'yan tawayen Abzinawa sun gobza faɗa a garin Kidal. Dama dai a 'yan kwanakinnan, an samu faɗace-faɗace nan da can, amma gobzawar ta jiya ita ce ta gaba da gaba mafi ƙarfi da aka samu tun watanni. Tun dai a ranar Alhamis ɗin da ta gabata ne, Abzinawa ƙarƙashin ƙungiyar MNLA, suka ce sun jingine jarjejeniyar da suka cimma da gwamnati, wanda aka yi tun a watan Juni. 'Yan tawayen sun zargi gwamnati Boubakar Keita da rashin cika ƙa'idar yarjejeniyar da suka cimma a baya. Tun bayan juyin mulki ne dai, 'yan tawayen Abzinawa da mayaƙan Islama suka ƙwace iko da arewacin Mali, kafin ƙasar Faransa ta kai farmakin ƙwato yankin.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Mohammed Nasiru Awal