1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon tashin hankali a Turkiya

August 28, 2014

A karon farko cikin watanni uku an samu hargitsi tsakanin 'yan sanda da masu zanga-zangar nuna ƙin jinin sabuwar gamnati a Turkiya.

https://p.dw.com/p/1D3MJ
Hoto: Reuters

Rahotanni daga ƙasar Turkiya na nuni da cewar jami'an 'yan sandan ƙasar sun yi amfani da hayaƙi mai sa hawaye domin tarwatsa masu zanga-zangar nuna adawa da sabuwar gwamnatin ƙasar. Zanga-zangar dai da cibiyoyin al'umma na ƙasar suka shirya, sun shiryata ne domin nuna adawa da sabon shugaban ƙasar Recep Tayyip Erdogan da aka rantsar da sanyin safiyar Alhamis ɗin nan. Wannan dai shi ne karon farko a cikin watanni uku da suka gabata a ƙasar aka samu wani sabon tashin hankali.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Abdourahamane Hasane