1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon tsinkayen IMF kan tattalin arzikin duniya

Becker, Andreas, Babayo/ SBJuly 20, 2016

Asusun ba da lamuni na duniya, IMF ko FMI, ya fitar da sabon tsinkaye bisa bunkasa tattalin arzikin kasashen duniya, lamarin ya shafi kasashen Afirka na Kudu da Sahara.

https://p.dw.com/p/1JSmJ
Deutschland Treffen Angela Merkel & internationale Finanz-Chefs
Shugabar Jamus tare da Shugabar Asusun ba da lamuni na duniyaHoto: Getty Images/AFP/J. MacDougall

Wannan tsinkaye ya duba yadda tattalin arzikin kasashen duniya zai kasance cikin wannan shekara ta 2016 da shekara mai zuwa ta 2017. Rahoton ya kuma duba halin da kasashen Turai suka samu kansu sakamakon kuri'ar raba gardama da 'yan Birtaniya suka kada na fita daga cikin kungiyar kasashen Tarayyar Turai da kasadar da yin hakan zai kasance ga tattalin arzikin kasashen gami da duniya baki daya. Maury Obstfeld da ke a matsayin daraktan asusun ba da lamunin na duniya, mai kula da sashen bincike ya yi karin haske:

"Yana da muhimmanci a duba hakikanin abin da zai faru bisa fitar Birtaniya daga Tarayyar Turai, a hada da batun tattalin arziki gami da rashin tabbas na siyasa da za a shafe watannin kafin sanin inda aka dosa. Duk wadannan abubuwa ne da suke kara bude kofofin da harkokin tattalin arziki ke mayar da martani mai fa'ida ko kuma akasin haka."

Nigeria Lagarde bei Buhari
Christine Lagarde da Shugaban Najeriya Muhammadu BuhariHoto: Reuters/A. Sotunde

Babbar matsalar za ta faru idan aka rasa samun mafita ta kirki tsakanin kasashen Turai da Birtaniya wajen fitar kasar daga Tarayyar Turai, abin da zai iya kara shinge kan harkokin kasuwanci, wannan shi ya sa asusun ya ce akwai yuwuwar tattalin arzikin duniya ya samu raguwa da kashi 0.6 cikin 100 a shekara mai zuwa, idan aka kwatanta da hasashen farko.

Wani abin da ya fito fili kan wannan rahoto shi ne kasashen Afirka na Kudu da Sahara sun samu gagarumi ragi kan bunkasan tattalin arziki da za a samu. Najeriya an rage bunkasa da za ta samu da kashi 4.1 cikin 100, saboda koma baya da tattalin arzikin kasar zai samu na kashi 1.8 cikin 100. Haka Afirka ta Kudu tattalin arzikin kasar ya tsaya cak. Sai dai Maury Obstfeld daraktan asusun ba da lamunin na duniya a sashen bincike ya ce akwai wasu matsalolin:

Christine Lagarde in Kenia
Christine Lagarde da shugaban kasar Kenya yayin da ta Kai ziyara a KenyaHoto: DW/A. Kiti

"Rage raguwar bunkasa tattalin arziki ga kasashen Afirka na kudu da Sahara ya faru saboda matsalolin da suka shiga habaka tattalin arzikin kamar a kasashen Najeriya da Afirka ta Kudu abin da ya sauya cikin hanzari. A shekara ta 2016 kasashen za su samu bunkasa wanda ya gaza da karuwar mutanen, lamarin da zai rage karfin tattalin arziki idan aka kwatanta da yawan mutane."

A gaba daya asusun na IMF ya ce, yanzu bunkasa tattalin arzikin duniya zai kasance kashi 3.1 cikin 100, zuwa kashi 3.4 cikin 100 a shekara mai zuwa. Haka ya nuna raguwar kashi 0.1 cikin 100 da aka yi tsammani ya zuwa watan Afrilu.