1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon yunkurin zaman lafiya a Dafur

April 15, 2007
https://p.dw.com/p/BuNf

A Gobe Litinin sakataren majalisar dinkin duniya Ban Ki-Moon zai bude taron shawarwari da kungiyar gamaiyar Afrika a game da rikicin Dafur wanda zai share fagen tura sojin kiyaye zaman lafiya na majalisar dinkin duniya zuwa yankin na kudancin Sudan. Ban Ki-Moon zai tattauna da shugaban hukumar hadin kan Afrika Alfa Omar Konare domin cimma yarjejeniya da gwamnatin Sudan na tura sojoji 2,300 na gamaiyar kasa da kasa domin dafawa dakaru 7,000 na kungiyar Afrika. Shugabanin biyu za kuma su mayar da hankali a kan matakin karshe na shawarar tura sojojin hadaka 20,000 na Afrika da kuma majalisar dinkin duniya domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Dafur. Ban Ki-Moon da Alfa Konare za su duba hanya mafi dacewa ta diplomasiya ta samar da zaman lafiya mai dorewa a Dafur. A goben dai har ila yau wakilin musamman na majalisar dinkin duniya a Dafur Jan Eliasson da takwaran sa na kungiyar Afrika Sali Ahmed Salim za su yi kokarin fadada yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Khartoum da yan tawayen Dafur a bara. A wani cigaban kuma kasar Libya ta sanar da karbar bakuncin taro wanda zai sami wakilcin kasashen Amurka da Britaniya da Chad da Sudan da Eritrea da kungiyar Afrika ta kuma kungiyar gamaiyar Turai don tallafawa rayuwar yan gudun hijirar Dafur.