1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabuwar alkiblar siyasa a kasar Masar

July 4, 2013

A daidai lokacin da aka rantsar da Adli Mansour a matsayin shugaban rikon kwarya a Masar, hambararren shugaban Masar Mohamed Mursi na karkashin daurin talala. Lamarin da ke janyo martani daga bangarorin daban-daban.

https://p.dw.com/p/192NW
Hoto: picture-alliance/AP

Yayin rantsuwar ta kama aiki, Adli Mansour dan shekaru 67 da haihuwa, wanda ya karbi madafun ikon kasar, ya yi alkawarin damawa da bangarorin al'ummomi daban-daban na kasar. Sabon shugaban ya yaba da yadda 'yan kasar suka yi tsayuwar tabbatar da neman 'yanci, da kuma jami'an tsaro wadanda suka tabbatar da kare al'uma cikin yanayi mai tsauri. Shugaba Adli Mansour ya samu digiri na farko kan fannin shari'a a jami'ar birnin Alkahira a shekarar 1967. Ya kuma samu babban digiri a fannin gudanar da mulki, wanda ya samu a shekarar 1970. Sannan ya yi karatu a makarantar horas da dabarun mulki ta kasar Faransa.

Sabanin ra'ayin duniya kan juyin mulki

Yanzu haka ana ci gaba da samun martani a kan juyin mulkin da sojojin kasar ta Masar suka jagoranta. Babban jami'in Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon, ya nuna rashin jin dadi da yadda sojojin suka yi katsaladan, inda ya ce hakan ya saba wa ka'idojin demokaradiyya. Amma a cikin kasar ta Masar mafi yawa na goyon bayan juyin mulkin. Hamdeen Sabahi na daya daga cikin 'yan takaran shugabancin kasar na bangaren 'yan adawa, inda ya ce "Ina tunanin cewa wannan dama ce ta bude, yadda za a gudu tare da tsira tare. Ya dace mu nuna hakuri da juna, wajen sasantawa na kasa, da duk bangarori ciki harda 'yan siyasa masu kishin Islama."

Ägypten Mursi Nachfolger Adli Mansour
Hoto: picture-alliance/AP

Maha Azzam masaniyar harkokin siyasar kasa da kasa ta yi gargadi a kan wannan juyin mulki na Masar; inda ta ce: "Sakon ya na da rikitarwa. Wannan ya nuna karara cewa masu kishin Islama da suka rungumi tafarkin demokaradiyya kuma suka shiga zabe, cewar idan kuka lashe zabe ba za mu kyale ku yi mulki ba. Sakamakon ya na da matukar hadari."

Matsayin kasashen Larabawa

Wannan faduwar gwamnatin Mursi ta zama gagarumin koma baya ga 'yan siyasa masu ra'ayin Islama, musamman ganin cewa kungiyar ta 'Yan Uwa Musulmai an kafa tun shekarar 1928, amma bayan kwashe shekara da shekaru ta na gwagwarmaya, mulkin shekara guda ta yi, bore al'uma ya janyo sojoji suka kawar da gwamnatin. Kuma irin wannan bore ne cikin shekara ta 2011 ya kawo karshen gwamnatin Hosni Mubarak ta shekaru 30.

Ägypten Mubarak Prozess Demonstration Tumulte Auseinandersetzungen Kairo Flash-Galerie
Hoto: picture alliance/dpa

Mafi yawan kasashen Larabawa sun yi maraba da kwace mulkin da sojojin kasar ta Masar suka yi daga hannun tsohon Shugaba Mohamed Mursi, yayin da kasashen Yammacin Duniya ke taka-tsantan tare da neman gannin an tsara hanyar mayar da kasar bisa tafarkin demokaradiyya cikin kankanin lokaci. Rahotanni sun ce kawo yanzu tsohon Shugaba Mohamed Mursi na karkashin daurin talala, bisa kulawar dakaru na musamman.

Mawallafi: Suleiman Babayo

Edita: Mouhamadou Awal

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani

Nuna karin labarai