1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabuwar hulda tsakanin Habasha da Iritiriya

Mohammad Nasiru Awal
July 13, 2018

Ganawa ta tarihi da aka yi tsakanin Firanministan kasar Habasha Abiy Ahmed da shugaban kasar Iritiriya Isaias Afwerki ta dauki hankalin jaridun Jamus.

https://p.dw.com/p/31Pq4
Äthiopischer Ministerpräsident Abiy Ahmed beim Staatsbesuch in Eritrea
Hoto: Twitter/@fitsumaregaa

A sharhin da ta yi mai taken dama ta tarihi, jaridar Süddeutsche Zeitung ta fara ne da cewa tsoffin abokan gaba sun rungumi juna lokacin wani taron koli na sulhu tsakanin Firaministan Habasha da shugaban Iritiriya a karshen mako. Jaridar ta ce kasashen biyu makotan juna sun shafe shekaru gommai suna gaba da juna, baya ga yake-yake da suka yi tsakaninsu da ya yi sanadi na rayukan mutane kimanin dubu 80. Amma farar daya komai ya canja tun bayan da Abiy Ahmed ya dare kan kujerar firaministan kasar Habasha a cikin watan Afrilu, ya kuma fara aiwatar da sauye-sauye cikin har da neman zaman lafiya da kasar Iritiriya. Jaridar ta ce yanzu dama ta samu ta wanzar da zaman lafiya a yankin kahon Afirka mai yawan al'umma fiye da miliyan 100.

Ita ma a sharhin da ta yi dangane da kokarin farfado da huldar dangantaka tsakanin Habasha da Iritiriya jaridar Zürcher Zeitung ta ce abin mamaki da yadda a cikin lokacin kankani aka fara ganin sauyi mai ma'ana na wani lamari da aka kasa gane kansa. Ta ce shekaru gommai Habasha da Iritiriya ke gaba da juna, da farko sun dauki tsawon lokaci suna gwabza mummunan rikicin neman 'yanci tsakanin 1998 zuwa 2000, sannan daga baya suka shiga yakin cacar baka. Yanzu sun kuduri aniyar wanzar da zaman lafiya tsakaninsu, kuma jim kadan bayan ziyarar da Firaministan Habasha Abiy Ahmed ya kai birnin Asmara na kasar Iritiriya, har an maido da layukan sadarwa ta waya tsakanin kasashen biyu, a cikin mako mai zuwa kuma kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Ethiopia Airlines zai fara sauka birnin Asmara. Kasashen biyu sun kuma maido da huldar diplomasiyya.

Bunkasar tattalin arziki a Afirka ba ta kawo wata wadatar a zo a gani ba, inji jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung tana mai ruwaito wani rahoto kann ci-gaba da kungiyar tarayyar Afirka da kuma kungiyar hadin kan tattalin arziki da ci-gaba suka wallafa a wannan makon a birnin Addis Ababa. Daga 2000 zuwa 2017 tattalin arzikin kasashe 55 na nahiyar Afirka ya samu bunkasa har ta kai wasu gwamnatoci a nahiyar sun kara kudi a ayyukan ci-gaban kasa. A wasu wuraren an rage yawan masu fama da matsanancin talauci. To amma bunkasar ta yi kadan ta yadda za ta inganta rayuwar mafi akasarin al’ummar nahiyar. Wata damuwar ita ce yawan marasa aikin yi musamman tsakanin matasa. Jaridar ta ce rage matsalar rashin daidaito na da muhimmanci a yaki da talauci.
 
A wani labarin kuma har wayau daga jaridar ta Frankfurter Allgemeine Zeitung ta ce albarkacin ranar bunkasar al’umma da ake yi a kowace ranar 11 ga watan Yuli, har yanzu nahiyar Afirka ke kan gaba wajen karuwar yawan al’umma a duniya. Jaridar ta ruwaito masana na cewa matukar aka cigaba a haka to ‘yan Afirka za su cigaba da yin kaura, wanda idan abin ya yi muni yana iya haddasa rikice-rikice, matsalar yunwa da ma annoba da za su taka wa bunkasar tattalin arzikin da nahiyar ke samu birki.