1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabuwar majalisar zartarwa a Gini

Nura Datti/ASJanuary 5, 2016

Masana na kallon sabuwar majalisar zatarwa da ke da mata wadda Shugaba Alpha Conde ya girka a matsayin kokarin farfado da tattalin arzkin kasar duba da kwararrun da ke ciki.

https://p.dw.com/p/1HYBd
Porträt - Alpha Conde
Hoto: picture-alliance/AP Photo/R. de la Mauviniere

Da dama a kasar ta Gini na yi wa wannan yunkuri na sanya kwararru a cikin jerin wanda ke cikin sabuwar gwamnatin da aka nada a Gini wani kokari na farfado da tattalin arzikin kasar wanda ya shiga wani yanayi maras kyau. Mutanen da ke cikin wannan sabuwar majalisar ta ministocin da yawansu ya kai goma sha shidda sun hada masanin harkokin hakar ma'adanai Mamady Youla a matsayin firainistan kasar.

Afrika Guinea Bissau Neue Regierung Gruppenbild
Sabuwar majalisar ministocin Gini ta sha banban da ta baya saboda kwararrun da ke cikinta.Hoto: Fátima Tchumá

Wani abu har wa yau da ya zama na ba sa banba a sha'anin kafa majalisar shi ne manyan mukamai masu gwabi da mata suka samu kamar ministar kula da tattalin arziki Malado Kaba yar shekaru 44 da haihuwa wadda ta kwase mafi yawan lokacinta ta na aiki a sashin kula da cigaban kasashe na Kungiyar Tarayyar Turai ta EU. Yawan matan da aka sanya a majalisar ministocin dai ba abu ne da aka saba gani ba musamman ma dai a nahiyar Afirka.

Ita ma dai ma'aikatar kula da harkokin kasashen ketare ta samu mace ne a matsayin wadda za ta jagorance kuma an mika wannan mukami ne ga Uwargida Makale Kamara wadda ta taba rike mukamin ministar harkokin noma a lokacin mulkin soja na shugaba Lansana Conte daga shekara ta 1984 zuwa shekara ta 2008, kana ta taba zama jakadiyar kasar ta Guinea a Faransa da kuma kasar Senegal.

Guinea Wahlkampf 2015
Lokacin yakin neman zabe Alpha Conde ya lashi takobin farfado da tattalin arzikin Gini.Hoto: DW/B. Barry

Fadar ta Shugaban kasar ta Gini Alpha Conde dai ta an bayar da mukamin na ministan kudi da tattalin arzikin ne ga kwararru da nufin farfado da tattalin arzikin kasar tare da kuma zummar tallafawa matasa da kuma inganta rayuwar masu karamin karfi.