1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon shirin DW game da nahiyar Afirka

Mohammad Nasiru AwalAugust 7, 2015

Muna mayar da hankali kan masu kawo canji, abin kuma koyi wadanda ke nuna kwazo da hazaka don ciyar da yankunansu da kuma nahiyar gaba.

https://p.dw.com/p/1GBkS
10.2015 Africa on the Move Teaserbild Haussa

Wani sabon zamani na matasan Afirka masu nuna kwarin guiwa wajen daukar makomarsu a hannu, wadanda kuma ke aiki tukuru wajen inganta rayuwa a nahiyar. Jerin shirye-shiryen na Sauyi a Afirka zai gabatar muku da gwarzayen Afirka da ke taka rawa a kyawawan abubuwan da ke faruwa a nahiyar. A cikinsu kuwa akwai kungiyar fafatuka a yanar gizo ta Oscibi, da ke zama bangaren kungiyar "Balai Citoyen" (The Citizen's Broom) a kasar Burkina Faso, wadda ta taka muhimmiyar rawa a fafatukar da ta kai ga "share" shugaban kasa na tsawon lokaci-Blaise Compaore daga ofis.

Jan hankali don taka rawa ta daban

Fanta Diallo mai fafatuka ce, kuma 'yar kasuwa da ke aiki don hana matasan Senegal daukar kasadar yin tafiya mai hatsari zuwa Turai. Tana taimaka musu suna samun sana'o'i masu amfani a gida. Sai kuma dan kasuwar kasar Ruwanda Serge Ndekwe, wanda duk da tsaiko da ya fuskanta daga 'yan siyasa, ya bude wani kasaitaccen gidan abinci da kuma wata masana'antar sarrafa madara. Wani matashi kuma dan kasuwar Afirka shi ne dan Afirka ta Kudu Calvin Phaala. Yana gabatar wa mazauna yankunan karkara sababbin fina-finai ta amfani da majiginsa kunshe cikin wata jakar goyo.

Dreharbeiten im Kongo für Africa on the move
Wakiliyar DW-Reporter Madelaine Meier da abokin aikinta Julien Adayé a Cote d'IvoireHoto: DW

Za a rika watsa rahotannin telabijin na "Sauyi a Afirka" a harsunan Ingilishi, da Kiswahili, da Hausa, da Faransanci da kuma harshen mutanen Portugal. DW za ta kuma gabatar da matasan da suka yi hobbasa a cikin shirye-shiryenta guda shida na rediyo ga Afirka da kuma kafofin sada zumunta.

Ku kasance da mu a shafin Facebook don gabatar mana da jarummanku da kuke gani za mu iya saka su a cikin jerin shirye-shiryen.