1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sahli: Ba jihadi na yi a kasar Faransa ba

Gazali Abdou TasawaJune 29, 2015

Yassin Salhi da ya kai hari a Faransa ranar Jumma'a ya ce abun da ya aikata na da nasaba ne da matsaloli na rayuwa da ya ke fama da su amma ba na addini ba ne.

https://p.dw.com/p/1FpnA
Frankreich Anschlag Ermittlungen
Hoto: Reuters/E. Foudrot

Mutumin nan mai suna Yassin Salhi da ake zargi da kai harin ta'addanci a kamfanin gaz na kasar Faransa ya ce danyen aikin da ya aikata ba shi da wata manufa ta kishin addini,kana shi ba dan jihadi ba ne. Ya bayyana haka ne ga masu bincike da suke yi masa tambayoyi tun bayan da aka kamashi.

Salhi ya ce abun da ya aikata na da nasaba ne da matsalolin rayuwa kawai da ya ke fama da su da suka hada da matsalar zama da matarsa. Sai dai masu bincike sun ce sun gano ya na da alaka da wani Bafaranshe mai da'awar jihadi da ya koma kasar Siriya da zama. Dama hukumomin leken asiri sun sha yin rijistansa a cikin jerin masu tsattsauran ra'ayin addini a shekarun baya bayannan ganin irin dangantakarsa da Salafiyawa na jihar Lyon.