1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakamakon farko na zaben Afghanistan

April 13, 2014

Tsohon ministan harkokin waje na Afghanistan Abdullah Abdullah ne ke kan gaba a kuri'un da aka fara kidayawa bayan kammala zaben shugaban kasa.

https://p.dw.com/p/1BhFF
Hoto: picture-alliance/dpa

Sakamakon farko na kuri'un da aka fara kidayawa bayan kammala zaben shugaban kasa a Afghanistan na nuni da cewa tsohon ministan harkokin kasashen ketare na kasar Abdullah Abdullah ne ke kan gaba, sai dai suna tafiya kusan kafada da kafada da abokin takararsa Ashraf Ghani.

Shugaban Hukumar Zaben kasar ta Afghanistan ta IEC Yousuf Nuristani ne ya sanar da hakan, inda ya ce daga cikin kaso 10 na kuri'un gundumomi 26 da suka kidaya Dr Abdullah ne ke kan gaba da kaso sama da 41 yayin da Dr Ashraf Ghani ke mara masa baya da kaso sama da 37 sai kuma Zalmai Rassoul dake da kaso sama da tara na kuri'un da suka kidaya.

Zaben kasar ta Afghanistan dai na zaman wani mataki na gwajin dorewar zaman lafiya a kasar, bayan janyewar sojojin kasashen ketare da suka kwashe tsahon shekaru a kasar.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Pinado Abdu Waba