1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakamakon shari'ar Khodorkovsky

December 28, 2010

Wata kotu a Rasha ta sami tsohon hamshaƙin mai kuɗin nan na Rasha Mikhael Khordorkovsky, da laifin aikata zamba da maguɗin kuɗi

https://p.dw.com/p/zqa3
Mikhael Khodorkovsky na tsakiyaHoto: AP

Hukuncin da wata kotu a Rasha ta yanke a kan wani hamshaƙin mai kuɗi wato Michael Khodorkovsky ya fara janyo cecekuce a tsakanin alummar ƙasa da ƙasa musamman ma Amurka da Ƙungiyar Tarayyar Turai. Ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle ya ce hukuncin abun damuwa ne sosai kuma babu shakka an tabka maguɗi wajen gudanar da shari'ar wanda hakan, ya nuna koma baya a hanun Rasha. Ƙungiyar Tarayyar Turai dai ta yi gargaɗin cewa zata sa ido a kan yadda Rasha zata zatar da hukuncin a kan Khodorkovsky, kuma Amurka ita ma ta ce hukuncin da Rasahar ta yanke, zai iya rage mata ƙima a idon alummar ƙasa da ƙasa.

A jiya litinin ne dai wata Kotu a Moscow ta yanke hukunci da ya sami Khodorkovsky, wanda ya taɓa zama mafi kuɗi a duk Rasha da laifin zamba da maguɗin kuɗi bayan da aka gurfanar da shi a gaban ƙuliya, a karo na biyu.

A yanzu haka dai Khodorkovsky yana gidan yari sakamakon wasu laifukan zamban da aka yi masa a baya.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu

Edita: Umaru Aliyu