1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakamakon Taron Jakarta

January 6, 2005

A taron da suka gudanar a Jakarta, fadar mulkin kasar Indonesiya a yau alhamis, dukkan mahalarta taron sun amince da danka wa MDD alhakin tafiyar da matakan taimako ga kasashen da bala'in Ambaliyar nan ta Tsunami ta rutsa da su

https://p.dw.com/p/Bvdm
Shugaban Indonesiya Yudhoyono
Shugaban Indonesiya YudhoyonoHoto: AP

Shugaban kasar Indonesiya Susilo Bambang Yudhayono da sakatare-janar na MDD Kofi Annan sune suka gabatar da jawabin bude taron na yau alhamis tare da gabatar da kakkarfan kiran taimako. Tun kuwa a ‚yan kwanakin da suka wuce ne kasashe ke ba da alkawururrukan taimako na dubban miliyoyin dala. Amma sakatare-janar na MDD Kofi Annan ya ce har yau ana bukatar karin taimakon kudi. Za a bukaci abin da ya kai dalar amurka miliyan dubu daya domin samar da ruwan sha mai tsafta da kayan masarufi da kuma magunguna ga mutanen da bala’in ya rutsa da su dangane da watanni shida masu zuwa. A baya ga haka za a bukaci wasu miliyoyi dubbai na dalar Amurka domin tallafa wa mutanen da suka yi asarar dukkan abubuwan da suke mallaka ta yadda zasu samu wata sabuwar madogara ga rayuwarsu ta yau da kullum. Shi kuwa shugaban kasar Indonesiya Susilo Bambang Yudhoyono ya fito fili ne ya bayyana cewar kasar ita kadai ba zata iya daukar nauyin sake gina yankunanta da ambaliyar ruwan ta bannatar ba. Sai ya kara da cewar:

A halin da muke ciki yanzu muna fuskantar wata matsala ce da ta biyo bayan wani bala’i daga Indallahi, wanda yayi sanadiyyar rayukan mutane sama da dubu 140 a baya ga wadanda ba a san makomarsu ba. Maganar nan da muke yanzu haka a wannan zauren ana ci gaba da tsintar gawawwakin mutane. Ita dai Indonesiya taba fuskantar bala’in fashewar wani dutse mai aman wuta da ya halaka mutane dubu 36 a 1883, amma ban taba tsammanin cewar a rayuwa ta zan taba shaidar da irin wannan bala’i, wanda adadin rayukan da suka salwanta ya ribanya wancan har sau uku.

Nan gaba za a yi wa kasashen dake gabar tekun Indiya damarar na’urar gangami akan kari, irin shigen wacce ke akwai a yankin tekun pacific. Kazalika taron ya tsayar da shawarar gabatar da wani sabon salo na taimako. Dukkan kasashen da bala’in ya shafa dai bashi ya kai musu iya wuya, a saboda haka mahalarta taron suka tsayar da shawarar sarara musu ta yadda kasashen zasu samu kafar sake gina yankunansu da ba’in yayi kaca-kaca da su. Wani abin lura a game da taron dai shi ne yadda MDD ta zama ja-gaba wajen jan akalar matakan taimakon. Majalisar ce za a danka wa alhakin raba kudaden taimakon da aka yi alkawurrrukan bayarwa da kuma manufifin da ya kamata a ba su fifiko. A dai mako mai zuwa idan Allah Ya kai mu kasashen G8 zasu gudanar da taro domin tattauna maganar saurara wa kasashen da bala’in ya shafa basussukan dake kansu.