1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugabanin EU sun ɗauki jerin matakai a birnin Brussels

Sadissou YahouzaJune 18, 2010

Shugabanin EU sun bayyana sabin matakan farfaɗo da tattalin arzikin ƙasashen Turai da kuma darajar Euro

https://p.dw.com/p/NuCo
Shugabanin ƙasashen EU a taro BrusselsHoto: AP

Shugabanin Ƙungiyar Tarayya Turai sun cimma daidaito, game da ɗaukar mataka bai ɗaya, na farfaɗo da tattalin arziki da kuma darajar takardar kuɗin Euro, wadda ta shiga wani mawuyacin hali.

A ɗaya wajen, shugabanin sun bayyana matakan riga kafi domin hana abukuwar irin wannan matsala dake barazana ga ƙasashen EU baki ɗaya.

A wani taron yini guda da suka shirya jiya  a birnin Brussels na ƙasar Beljiam shugabanin ƙasashen EU sun yanke shawara gudanar da binciken ƙwaƙwaf ga bankuna ta yadda za a fayyace shigi da fici kuɗaɗe.

Ƙungiyar Tarayyar Turai ta bayyana cewar, za ta shawarci ƙungiyar ƙasashen da suka ci gaba a fannin masana'antu ta G20, ta ɓullo da haraji akan cibiyoyin kuɗi da bankuna domin shawo kan matsalolin da sashen ke janyowa harkokin tattalin arziƙin ƙasashe.

Daga jerin matakan da ta ɗauka a taron Brussels,  Ƙungiyar Tarayya Turai, ta amincewa ƙasar Estoniya ta shiga rukunin ƙasashe masu amfani da takardar kuɗin Euro daga 1 ga wata Janairu na shekara ta 2011.Estoniya zata kasance ƙasa ta 17 dake amfani da kuɗin Euro.

Mawwallafi: Yahouza Sadissou Madobi Edita: Zainab Mohamed Abubakar