1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakamakon zaben fidda gwani a Iowa

Yusuf Bala/GATFebruary 2, 2016

A Amirka Sanata Ted Cruz da Hillary Clinton sun samu nasarar zabukan fiddan gwani na farko da ya gudana don fidda dan takarar shugabanci kasa a jam'iyyunsu na Republican da Democrat

https://p.dw.com/p/1HnNB
US Wahlen Parteikonferenz in Iowa Caucus Hillary Clinton
Hoto: Reuters/A. Latif

A cewar ofishin kula da yakin neman zaben Hillary Clinton wadda ke neman tsayawa takarar shugaban kasar Amirka ta Amirka karkashin inuwar jam'iyyar democrats, ta sanar a yau Talata, cewar sune suka yi nasara a zaben fidda gwani da aka yi a jihar Iowa. Da take magana wa taron magoya bayanta 'yar takara Hillary Clinton ta ce.

"Na san da za mu iya kirkiro da ayyukan ma su kyawawan albashi, tare da kyautata rayuwar Amirkawa masu ayyuka tukuru. Na san da muna iya karasa ayyukan da aka soma na iganta kiwon lafiyar dukannin al'umma maza da mata da yara kanana."

Cikin wata sanarwa ce dai kafin sakamakon fidda gwanin ya fito, daraktan yakin neman zaben na Cliton, Matt Paul, ya ce babu wata tantama 'yar takararsu ce ke da mafi yawan wakillai na jihar da ma na kasa baki daya. Hilary Clinton dai ta yi kusan kankankan ne da Bernie Sanders.

US Wahlen Parteikonferenz in Iowa Caucus Ted Cruz
Hoto: picture-alliance/dpa/C. Lassig

Shi kuwa dan takarar shugabancin Amirka karkashin jam'iyyar Republican Ted Cruz wanda ke zama kan gaba a zaben fidda gwani da aka yi a jihar ta Iowa, shi ma ya bayyana nasarar da ya samu da cewa wata dama ce ga 'yan ra'ayin rikau, kuma wata alama ce da ke nuna cewa kafafen yada labarai ba su ne za su zabi shugaban kasar Amirka ba.

"Al'ummar Iowa sun aika da sakon cewa, dan takarar shugabancin Amirka karkashin jam'iyyar Republican, kuma shugaban Amirka na gaba ba kafafen yada labarai za su zabe shi ba".

Sanata daga jihar Texas Cruz da a karon farko ya samu kashi 28 cikin dari, inda ya sha gaban dan takarar shugabancin karkashin jam'iyyar ta Republican da ake ta cece-kuce a kansa Donald Trump wanda ya samu kashi 24 cikin dari.

Wannan jiha ta Iowa dai na da muhimmanci a zaben na Amirka, wacce kan zama 'yar manuniya ga irin rawar da 'yan takarar za su taka a sauran jihohin na Amirka. Jihar New Hampshire, na zama ta gaba da hankali zai koma a kanta, wacce za a yi zaben na fidda gwani a ranar tara ga watannan na Fabrairu.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani