1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakataren harkokin wajen Amurka na yin ziyara a Gabas ta Taskiya

April 7, 2013

Wannan ita ce ziyara ta uku da jagoran diflomasiyyar na Amurka ke yi a cikin wata guda a yankin domin tattauna rikicin Siriya da na Falasɗinu da Isra'ila.

https://p.dw.com/p/18B9q
US Secretary of State John Kerry (R) delivers remarks to US Foreign Serivce workers on April 7, 2013 during a early morning meeting regarding the death of a fellow US Foreign Service worker in Zabul province, Afghanistan, as US Ambassador Francis Ricciardone (L) attends in Istanbul. Kerry arrived on April 7 in Turkey to discuss Syria's civil war and the Middle East peace process as well as to bolster the Turkish-Israeli rapprochement brokered two weeks ago by Washington. AFP PHOTO POOL /PAUL J. RICHARDS (Photo credit should read PAUL J. RICHARDS/AFP/Getty Images)
Hoto: Paul J. Richards/AFP/Getty Images

Sakataran harkokin wajen Amurka John Kerry ya soma wata ziyarar aiki a wannan Lahadi a ƙasar Turkiya. A wani mataki na rangadi na kwanaki goma da zai yi a cikin ƙasashen Gabas ta Tsakiya da Ingila da Japan da kuma yankin Asiya.

Muhimman bututuwan da babban jami'in diflomasiyyar na Amurka zai mayar da hankali a kansu a lokacin ziyara, shi ne zancen tashin hankalin da ake yi a Siriya da rikicin Koriya ta Arewa da kuma na yankin Gabas ta Tsakiya tsakanin Israi'la da Falasɗinu. Masu lura da al'amuran yau da gobe na furta kalamun cewar Amurka ta zaɓu wajen ganin an shawo kan rikicin na yankin Gabas ta Tsakiya, ta hanyar sake farfaɗo da shirin tattaunawa na gaba da gaba tsakanin Falasɗinu da Isra'ila.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane

Edita : Mohammad Nasiru Awal