1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin sakin wasu 'yan fafaren hula na Jamhuriyar Nijar

Suleiman Babayo USU
May 1, 2020

Ana ci gaba da mayar da martani kan matakin gwamnati Jamhuriyar Nijar na saki manyan shugabannin kungiyoyin fararen hula guda biyu ayayin da sauran suke ci gaba da zama a tsare.

https://p.dw.com/p/3bf0h
Moussa Tchangari, Journalist und Menschenrechtler
Moussa TchangariHoto: DW/ Thomas Mösch

Wata kotu a birnin Yamai na jamhuriyar Nijar ta ba da bailin wasu 'yan fararen hula biyu Moussa Tchangari shugaban kungiyar Alternative Espace Citoyen da Habibou Moussa na kungiyar Tournons la Page, gami da shugaban 'yan kasuwa masu shigo da fitar da kayayyaki na kasar Alhaji Sani Chekarau bayan da suka shafe tsawon kwana ki 45 a gidajen kaso dabam-dabam na kasar ta Nijar.

Sai dai kuma sauran 'yan kungiyoyin fararan hula da suka hada da Maikol Zody, Moudi Moussa wanda dan jarida ne, da kuma Mounkaila Halidou shugaban kungiyar Maluman Makaranta ta CYNACEB an yi watsi da neman yi musu sakin talalan da lawyoyinsu suka shigar.