1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Salon shugabancin sabon jagoran Taliban

November 7, 2013

Sabon shugaban Taliban Mollah Fazlullah ya yi fatali da tayin da gwamnatin Pakistan ta yi musu na zama kan teburin tattaunawa domin sulhunta rikicin da ke tsakaninsu.

https://p.dw.com/p/1ADsb
A Pakistani journalist watches a newly released video of radical Pakistani cleric Maulana Fazlullah in Peshawar on July 23, 2010. A newly released video of what appeared to be fugitive radical Pakistani cleric Maulana Fazlullah shows him firing gunshots and addressing a group of suicide bombers. Fazlullah mounted a violent two-year campaign to enforce Islamic sharia law in the northwestern district of Swat, opposing education for girls and beheading opponents until the government ordered in thousands of troops. AFP PHOTO/ A. MAJEED (Photo credit should read A. MAJEED/AFP/Getty Images)
Hoto: A. Majeed/AFP/Getty Images

'Yan Taliban na kasar Pakistan sun nada wanda ake zargi da kai wa Malalah Yousafzai hari wato Mollah Fazlullah a matsayin sabon shugaban kungiyarsu. Ana dangantashi da wanda ya saba amfani da kafar rediyo wajen yin zafafan hudubobi da kuma kwarewa a fannin gagwarmaya da makamai. Sannan kuma shi Mollah Fazlullah ne ya kafa shari'ar Musulunci daga shekara ta 2007 zuwa ta 2009 a tuddan Swat.

Sai dai kuma Mollah Fazlullah ya sa kafa ya yi fatali da tattaunawar samar da zaman lafiya da ake shirin yi tsakanin gwamnati da masu tsattsauran ra'ayin Islama. Kakakin Fazlullah ya bayyana wa manema labarai cewar, gwamnatin Pakistan da ke ci a yanzu ba ta da hurumin tattaunawa dasu saboda haramtacciya ce. Wannan ya zo ne kasa da mako guda bayan da Amirka ta yi amfani da jirgin da ke sarrafa kansa da kansa wajen kashe tsohon jagoran Taliban a Pakistan wato Hakkimullah Mehsud.

Gwamnatin ta Pakistan ta na kokarin shawo kan kungiyar Taliban da ta ajiye makamai domin kawo karshen rikicin da ya daidaita kasar da ta kunshi mutane miliyan 180.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Saleh Umar Saleh