1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bakin haure 500 sun kubuta a Libiya

Yusuf Bala Nayaya
August 1, 2018

Dakarun da ke lura da gabar teku a Libiya sun ceto bakin haure 574 cikin wasu jiragen ruwa marasa inganci a wani aiki da suka fita a ranar Litinin a wajen gabar tekun kasar da ke a arewacin Afirka.

https://p.dw.com/p/32TMv
Libyen schiffbrüchige Migranten im Mittelmeer ertrunken
Hoto: Getty Images/AFP/M. Turkia

Ayoub Qassem da ke magana da yawun sojan ruwan kasar ta Libiya ya bayyana labarin kubutar da mutanen ga kamfanin dillancin labaran Reuters.

Ya ce cikin bakin hauren akwai maza 388 da mata 66 da yara 16. Jiragen ruwa biyu ne aka gansu ba nisa da garin Zawiya da wani jirgin a kusa da Qarabulli. Qassem ya ce bakin hauren sun fito ne daga kasashen Afirka dabam-dabam.

An dai samu raguwar bakin haure da ke barin gabar tekun a Libiya tun daga shekarar 2017 a kokarin da suke yi na gudun talauci da yake-yake da neman ingantacciyar rayuwa a Turai.