1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Littattafan yaki da Boko Haram a Chadi da Kamaru

Abdul-raheem HassanJune 8, 2016

Marabuta suna samar da mafita ga yara kan yaki da matsanancin ra'ayi irin na Boko Haram a kasashen Kamaru da Chadi.

https://p.dw.com/p/1J2Vk
Kamerun Flüchtlingslager Minawao
Hoto: AFP/Getty Images/R. Kaze

Marubuta littattafai a kasar Chadi da Kamaru, sun amince da wallafa littattafai da za su koyar da nuna akidar kungiyar Boko Haram ga daliban makarantun Firamare. Nazarin marubutan na a matsayin gudumuwa ce da zai ceto yara kanana fadwa akidun ta'addanci.

Marubutan sun yi amfani kada-kade wajen tattara hankalin Hausawa da ke babban birnin Kamarun wato Yawunde. "Hausa Quaters" dai sanannen mafaka ne da ya tara dubban 'yan gudun hijiran da rikicin Boko Haram ya raba da matsugunansu daga Arewacin Kamaru da Chadi. Wadannan mawallafa sun kuma rera baitukan jan hankali da isar da sako ga mutane daga cikin littattafan akwai "No Terrorism" wato babu ta'addanci wanda marubuci Kamaru Christian Ngange ya wallafa.

Symbolbild Afrika Kinderbräute
Hoto: picture alliance/AP Images/S. Alamba

Yunkurin wadannan marubuta dai, shine na ganin sun kaste dabarun da mayakan ke amfani da su wajen dasa akidar ayyukan ta'addanci. Renaud Dinguemnaial marucin kasar Chadi ne da ke ganin irin wadanan littattafai na nuna hannun riga da akidar 'yan Boko Haram.

A yunzu dai, gwamnmatin Kamaru da Chadi sun amince da a sirka wadannan littattafai a makarantu a matsayin darusa na farko da za a nuna wa yaran da ke zuwa makarantu illolin akidun kungiyoyin ta'addanci. Wata dalibar jami'a 'yar shekaru 19 Alvine Ngah, tana cikin wadanda wadannan littattafai ya fitar cikin duhu matuka.

Niger Binnenflüchtlinge Flüchtlinge Vertriebene Nigeria
Hoto: Getty Images/AFP/B. Hama

Sama da shekaru 7 ke nan kasashen Kamaru, da Chadi, da Najeriya da kuma Jamhuriyar Benin ke yaki dar mayakan Boko Haram. Sai dai amincewa a yi amfani da wadannan littattafai da wasu gwamnatoci suka yi a makaratu, zai sa yara su tsira daga tarkon mayakan na Boko Haram.