1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Samun galaba a kan Boko Haram

Lateefa Mustapha Ja'afarSeptember 25, 2014

Rundunar sojoji a Tarayyar Najeriya ta sanar da cewa daruruwan 'yan kungiyar Boko Haram sun mika makamansu ga jami'an tsaro.

https://p.dw.com/p/1DKkm
Hoto: dpa

Kakakin rundunar sojojin kasar Janar Chris Olukolade ne ya sanar da hakan ga manema labarai a Abuja, fadar gwamnatin Tarayyar ta Najeriya, inda ya ce 'yayan kungiyar ta Boko Haram sun mika makaman nasu ne a garuruwan Biu da Mairiga da Buni Yadi da Mubi da kuma Michika. Haka nan ma ya ce wasu sun mika makaman ga jami'an tsaro a makobciyar Najeriyar wato kasar Kamaru. Olukolade ya kuma tabbatar da cewa sun hallaka wanda ya ke bayyana a faifen Video a matsayin shugaban kungiyar ta Boko Haram Abubakar Shekau mai suna Mohammed Bashir, yayin wata arangama da sojojin suka yi da 'yan kungiyar a garin Konduga dake kimanin kilomita 35 da garin Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno, a tsakanin ranakun 12 zuwa 17 ga wannan wata na Satumba da muke ciki. Dubun dubatar rayuka ne dai 'yan kungiyar ta Boko Haram suka hallaka a Tarayyar Najeriyar ta hanyar kai hare-haren ta'addanci da bama-bamai da kuma manyan bindigogi.