1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sanarwar Schröder Akan Manufofin Gwamnatinsa

April 30, 2004

Dukkan gwamnati da 'yan hamayya na doki da murna a game da karbar sabbin kasashe goma na tsakiya da gabaci da kuma kudu-maso-gabacin Turai a Kungiyar Tarayyar Turai

https://p.dw.com/p/Bvk5
Schröder na gabatar da sanrwa akan manufofin gwamnatinsa game da KTT
Schröder na gabatar da sanrwa akan manufofin gwamnatinsa game da KTTHoto: AP

Yau dai rana ce ta farin ciki da murna tsakanin gwamnati da ‚yan hamayya a majalisar dokokin Jamus ta Bundestag. Domin kuwa bikin da ake shirin gabatarwa a game da karbar sabbin kasashe na tsakiya da gabaci da kuma kudu-maso-gabacin nahiyar turai a Kungiyar Tarayyar Turai wani babban ci gaba ne na tarihi a cewar shugaban gwamnati Gerhard schröder a cikin sanarwar da ya bayar dangane da manufofin gwamnatinsa a majalisar dokokin. Schröder ya kara da cewar:

Sama da mutane miliyan 45 ne suka yi asarar rayukansu sakamakon yake-yaken duniya guda biyu da aka fuskanta a nahiyar Turai. Ta la’akari da haka matsaloli na tattalin arziki da na haraji da aka rika tafka mahawara kansu, ko da yake suna da muhimmanci, amma fa a hakika ba a bakin kome suke ba idan aka kwatanta da wannan ci gaba na tarihi da aka samu.

Su ma ‚yan hamayya suna tattare da imanin cewar karbar sabbin kasashen guda goma a Kungiyar tarayyar turai wata kyakkyawar dama ce da zata kai ga bunkasar tattalin arziki da kyautata zaman cude-ni-in-cude-ka a nahiyar Turai. An saurara daga bakin shugabar jam’iyyar CDU Angela Merkel tana mai yin nuni da cewar wannan muhimmin ci gaba ne aka samu a kan hanyar hadin kan nahiyar Turai, lamarin da zai kai ga bunkasar siyasa da tattalin arziki da al’amuran al’adu a wannan nahiya. To sai dai kuma a nasa bangaren shugaban gwamnati Gerhard schröder ya ce ko da yake wannan ci gaba ne dake ba da kwarin guiwa bisa manufa, amma kuma abu ne dake tsorata da yawa daga Jamusawa. Mutane masu tarin yawa a nan kasar na fargaba a game da makomar guraben ayyukansu sakamakon karbar sabbin kasashen guda goma a KTT. Abin takaici shi ne yadda wasu marasa halin sanin ya kamata ke amfani da wannan fargaba domin kara jefa mutane cikin hali na rudu da rashin sanin tabbas game da makomarsu. Shugaban gwamnatin na Jamus ya kara da gabatar da gargadi ga ‚yan kasuwa a game da wani yunkuri na shiga gasar karancin albashin ma’aikata da sabbin kasashen na KTT. Jamus ce zata dandana kudarta a irin wannan gasa. Amma bisa ga ra’ayin Angela Merkel shugabar CDU irin wannan gasar ka iya daukar wani fasali na aiwatar da garambawul ga tsarin albashin ma’aikata ta yadda ba za a yi asarar guraben aikin yi ga jama’a ba. Ta ce muhimmin abu shi ne kungiyar ta rika magana da murya daya. Shi ma ministan harkokin waje Joschka Fischer ya bayyana ra‘ayin cewar daftarin tsarin mulki bai daya da aka zayyana ka iya zama tushen wannan hadin kai. Har yau dai ana ci gaba da sabani tsakanin gwamnati da ‚yan hamayya a game da karbar kasar Turkiyya a KTT. A yayinda gwamnati ke neman ganin an gabatar da matakin shawartawa a game da karbar Turkiyyar a kungiyar, su kuma ‚yan hamayya gani suke cewar lokacin yin hakan bai yi ba tukuna.