1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sanders daTrump sun lashe zaben New Hampshire

Zainab Mohammed AbubakarFebruary 10, 2016

Zaben fidda da gwani a karamar jihar New Hampshire na zama zakaran gwajin dafi na share hanyar zuwa fadar gwamnatin Amurka ta white house.

https://p.dw.com/p/1HsSX
USA Bernie Sanders Donald Trump Kombo
Hoto: Reuters/DW Montage

Dan takarar kujerar shugabancin Amurka Bernie Sanders ya doke Hillary Clinton a New Hampshire a zaben fidda gwani na jam'iyyar Demokrats. Dan majalisar dattawan na Amurka da ke wakiltar Vermont, wanda ya bayyana kanshi da dan demokradiyya mai sassaucin ra'ayi ya yi kira da a kawar wasu nau'oi na nuna banbanci a fannin harkokin kudi, wanda zai karya manyan bankuna tare da samar da ilimin kwaleji kyauta.

"Cikin 'yan watanni masu gabatowa muna bukatar hada kawunanmu, hada kan wannan jam'iyya da ma wannan kasa tamu. Kasancewar ba zai dace mu bawa 'yan Republican da me adawa da su damar mamaye kujerar shugabanci ba".

A bangaren jam'iyyar Republikan kuwa, hamshakin dan kasuwa Donald Trump ya doke abokin takararsa kai tsaye. Da samun kashi 33 daga cikin 100, ya doke abokan takararsa dan majalisar dottawa da ke wakiltar Texas Ted Cruz da gwamnan Florida Jeb Bush. Zaben fidda da gwani a wannan karamar jiha da ke yankin Arewa maso Gabashin kasar dai, na zama wani zakaran gwajin dafi ne na share hanyar zuwa fadar gwamnatin Amurkan ta White House.