1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sarauniya Muhumusa: Yakar mulkin mallaka a gabashin Afirka

Lateefa Mustapha Ja'afar USU
July 25, 2018

Kimanin shekaru 100 da suka gabata a Yuganda, wata mata ta tashi tsaye domin yakar Turawan mulkin mallaka. Ta kasance gwanar sihiri, shugabar sojoji kana mai yakar rashin adalci.

https://p.dw.com/p/2udF6
African Roots Muhumusa
Hoto: Comic Republic

Ta rayu: 

Duk da cewa ba a san takamaimiyar ranar da aka haifi sarauniya Muhumusa ba, sai dai tarihin rayuwarta ya samo asali tsakanin karni na 18 da na 19. Ita ce mai dakin sarkin Ruwanda, Sarki Kigeli na IV. Lokacin da mijinta ya rasu a shekara ta 1895, aka kuma hana danta ya gaje shi, ta yaki tsarin shugabancin Ruwanda da kuma Turawan mulkin mallaka. Ta koma Yuganda, Turawan mulkin mallaka na Birtaniya sun sha kama ta, sun kuma tsareta a Mengo, inda ta rasu a shekara ta 1945. Ba ta sake samun dama ta koma kasarta ba.

 

An san ta da: 

Ta samu sihirinta daga fitacciyar sarauniya a Afirka wato Sarauniya Nyabingi. Turawan mulkin mallaka sun bayyana ta a matsayin "mai abin al'ajabi." Da dama daga mabiyanta ba su taba ganin fuskarta ba, kasancewar sihirinta ya bukaci ta rinka buya a cikin kwando.

Muhumusa

Ana mutunta ta: 

Ta yaki Turawan mulkin mallaka daga kasashen Jamus da Birtaniya da kuma Beljiyam. Ta kuma yi tirjiya ga al'adu da kuma tsarin da ke take hakkin mata.

 

Cece-kuce: 

Wasu mabiyanta sun yi imanin cewa ita ce Sarauniya Nyabingi. Wasu kuma na ganin sake haifarta aka yi ko kuma fatalwar sarauniyar Ruwanda da ta rayu a wasu karnuka da suka gabata ta dawo. Abin takaici babu cikakken tarihinta sakamakon rashin mai da hankali na al'umma da kuma illar mulkin mallaka.

 

Abin tunawa: 

Masu yakar mulkin mallaka a kasashen Ruwanda da Yuganda na koyi da ita. A yanzu mabiyanta na ganinta a matsayin abar koyi kuma abar girmamawa a cikin al'umma. Tasirinta ya ci gaba da yaduwa tsakanin mutanen da ke da akida ta Rasta.

 

Jane Ayeko-Kümmeth da Philipp Sandner sun taimaka wajen hada wannan tarihin. Wannan wani bangare ne na shiri na musamman na tashar DW mai taken "Tushen Afirka" da hadin gwiwar gidauniyar Gerda Henkel ta Jamus.