1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saudiyya da Iran ana takaddamar harba makami

Yusuf Bala Nayaya
November 7, 2017

Wannan dai na zuwa ne bayan da wani makami mai linzami daga Yemen ya fada Saudiyya, abin da ta ce da hannun Iran a ciki.

https://p.dw.com/p/2nEAm
Archiv Saudia Arabien Spezialeinheit Polizei
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Nelson

Kasar Iran ta yi watsi da zargin mahukuntan birnin Riyadh na Saudiyya wacce ke zarginsu da hannu bayan da wani makami mai linzami ya fada kasar ta Saudiyy daga makociyarta Yemen. Makamin dai da aka harba a karshen mako ya nufi birnin Riyadh ne fadar gwamnatin Saudiyya.

Yarima Mohammed bin Salman na kasar ta Saudiyya ya ce kasar ta Iran ta bawa mayaka na Houthi makami mai linzami a Yemen don su harba Saudiyya, kuma wannan takala ce da ba za su lamunta ba kamar yadda kamfanin dillancin labarai a Saudiyya ya nunar.

Shi ma dai ministan harkokin wajen Iran Bahram Ghassemi a wannan rana ta Talata ya mayar da martani inda ya ce zargi ne kawai mara tushe ballantana makama, abin da kuma zai iya harzuka mahukuntan na Tehran.