Senegal: Jin duriya ta karshe

Now live
mintuna 03:55
Ali Koury da ya rasa dansa a cikin 'matasan Senegal da ke kaura zuwa Turai, ya kafa wata kungiya ta wadanda suka bace.

Thiaroye-sur-mer kauyen masunta a Senegal na da tarihin da ke bata rai: Sama da matasa 500 a nan suka fice zuwa Turai. Sai dai tun lokacin da suka tafi ba wanda ya dawo daga cikinsu, abinda ya sa ake daukar cewar sun bace. Ali Koury da ya rasa dansa a cikin wannan lamari, ya kafa wata kungiya ta wadanda suka bace.