1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Senegal ta kira jakadanta a Katar zuwa gida

Gazali Abdou Tasawa MNA
June 7, 2017

Senegal ta kira jakadanta a Katar da ya dawo gida a wani mataki na nuna goyon baya ga matakin Saudiyya  da wasu kasashen Larabawa na katse huldar diplomasiyyarsu da Katar a bisa zargin tallafa wa ta'addanci.

https://p.dw.com/p/2eHik
Senegals Präsident Macky Sall im DW-Interview in Dakar
Hoto: DW/A. Kriesch

Kasar Senegal ta sanar da cewa ta bukaci jakadanta a kasar Katar da ya dawo gida a wani mataki na nuna goyon baya ga matakin kasar Saudiyya  da wasu kasasashen Larabawa na katse huldar diplomasiyyarsu da kasar ta Katar a bisa zargin tallafa wa kungiyoyin 'yan ta'adda da yin katsalandan a harkokin cikin gidajensu da kuma yin mu'amala da kasar Iran. 

A cikin wata sanarwa da ministan harakokin wajen kasar ta Senegal ya fitar a wannan Laraba, ya ce sun bukaci jakadan nasu da ya dawo gida har zuwa yadda hali ya yi a nan gaba. Sanarwar ta kara da cewa kasar Senegal ta damu sosai da halin da ake ciki a yankin Golf, dan haka take goyon bayan matakin da kasashen Saudiyya daMasar da Bahrain da Daular Larabawa suka dauka na raba gari da kasar ta Katar. 

A ranar Litinin da ta gabata ce dai kasashen hudu suka katse huldar diplomasiyyar tasu da kasar Katar kafin daga bisani kasashen Yemen da Mauritaniya da kuma Maldibas su bi sahunsu wajen raba gari da Doha.