1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shagulgulan ista cikin fargaba a Najeriya

April 18, 2014

A yayin da mabiya addinin Krista ke bubukuwan Ista a tarrayar Najeriya, matsalar rashin tsaro ta haifar da zaman dar-dar a birnin Abuja da kuma jihohin arewacin kasar da ke fuskantar wannan kalubale.

https://p.dw.com/p/1Bkta
Anschläge auf Kirchen in Nigeria Afrika ARCHIV
Hoto: picture-alliance/dpa

Rashin tsaro ya kara daukan sabon salo ne biyo bayan harin bom da aka kai a farkon makon nan a Abuja wanda ya zo dab da bikin Ista. Walwalar da aka saba ta kasance takaitaciyya, abin da ke rage armashin bikin. Ganin irin zaman tankiyar da ake yi, ya sanya wani kirista da ke zama a Abuja ya shaida wa DW cewa "Mutane da dama sun so su yi tafiya amma sun kasa yin hakan, kuma ba komai ya hanasu ba sai don yanayin tsaro. A gaskiya mutane sun na cikin hali na dar-dar''.

Kirche Nigeria
Kirostocin arewacin Najeriya ma na fargabar tashin hankaliHoto: picture-alliance/dpa

Sai dai jami'an tsaro sun bayyana cewa al'ummar birnin Abujan su saki jikinsu domin kuwa sun dauki matakan tabbatar da cewa an yi bikin Ista an gama lafiya. Don haka ne ma ake ta kakkange wurare da dama musamman na ibada kamar yadda jami'ar yada labaru ta hukumar ' yan sanda Najeriya DSP Hilleria Altine Daniel ta bayyana.

‘'Mu a rundunar ‘yan sanda na nan Abuja mun kara daura damara mu tabbatar da cewa an ci gaba da samun wanzuwar zaman lafiya, don mun dauki matakan tsaro sosai, ina mai tabbatar masu cewa mun dauki matakan kare lafiyarsu da dukiyarsu, don haka su fita su je su shakata . In jama'a sun ga wani abinda ba su gane ba to su sanar damu don mu dauki mataki a kai''.

Amma ga Hon Peter Gumtha matsalar rashin tsaron ba wai kamata ya yi a mai da hankali a kan Abujan ba ne kadai, domin a arewa maso gabashin Najeriya da aka fi fama da hare-hare ya kamata a magance matsalar. Wannan sabon yanayi da birnin Abujan ya shiga dai ya sauyashi daga birnin da aka sani mai cike da zaman lafiya, kwanciyar hankali da ma cikakken tsaro musamman saboda kasancewarsa cibiyar gwamnatin Najeriya. To sai dai sannu a hankali wannan ya sauya, inda matsalar kai hare-haren da ake fuskanta a wasu jihohin kasar ta yi nasu zuwa birnin.

Nigeria - Kanduna
Jami'an tsaro sun yi alkawarin kare kiristoci daga hare-hareHoto: Getty Images

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris daga Abuja
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe