1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

D EU Drogensituation

November 11, 2010

Raguwar amfani da hodar Iblis da ƙaruwar wasu miyagun ƙwayoyin tsakanin matasa

https://p.dw.com/p/Q6VI
Hoto: AP

Idan ana batun miyagun ƙwayoyi dai akan danganta shi da hodar Iblis da dangoginta. Sai dai ana iya cewar ana samun koma baya dangane da tafiyar da kasuwancin waɗannan miyagun ƙwayoyi. Yanzu haka dai an fi amfani da wasu ababan maye da suka haɗar da ƙwayoyi da dangoginsu. Waɗanda ke da sauƙin samu, sai dai a hannu guda kuma suna da haɗarin gaske, akasarin matasan dake shan su basu san illolin dake tattare da su ba.

Waɗannan bayanai dai suna ƙunshe ne a cikin rahoton shekara ta 2010 da babbar jami'ar yaƙi da miyagun ƙwayoyi a Jamus Mechthild Dyckmans da cibiyar nazarin ƙwayoyin Turai suka gabatar a ranar Alhamis.

Kimanin mutane miliyan huɗu ne dai rahoton ya kiyasta cewar suna shan irin waɗannan miyagun ƙwayoyi a nahiyar Turai. Cibiyar yaƙi da miyagun ƙwayoyin ta Turai ta yi nuni da cewar, kokain ya kasance tamkar tsohon ya yi a wajen masu hannu da shuni. Sai dai har yanzu tabar Wiwi na da rinjaye a kasuwannin bayan fage.

Ana noman ganyen tabar Wiwi ɗin ne a yankin arewacin Afirka, kazalika da nahiyar Turai. Inda masu bincike ke cigaba da nazarinsa, a cewar Wolfgang Götz na cibiyar binciken miyagun ƙwayoyi da masu shan su na nahiyar Turai.

"Ba wai ina hasashe kawai ba ne ko kuma abu makamancin haka. Ina batu ne dangane da 'yan shekaru da suka gabata, sadoda ƙaruwar sarrafa shi a yammacin Turai. Kuma ina magana ne dangane da ƙaruwar noman ganyen tabar Wiwi"

Symbolbild Heroin
Hoto: picture-alliance / dpa

Sai dai duk da haka ba a samu ƙaruwar yawan waɗanda ke shan waɗannan miyagun ababan mayen a bayan fage ba. A faɗin duniya baki ɗaya dai ana samun koma baya wajen shan tabar Wiwi kamar yadda rahoton Majalisar Ɗunkin Duniya yayi nuni da shi. Kana a nan tarayyar Jamus ana samun koma baya na shan miyagun ƙwayoyi tsakanin matasa.

Sai dai ba za a iya cewar matsalar ta kau gaba ɗaya ba, saboda a yayin da ake ƙokarin yaƙi da sha ko kuma fataucin waɗannan miyagun ƙwayoyi tsakanin matasa, hanyoyin sadarwa na zamani kamar yanar gizo na taka muhimmiyar rawa wajen jan hankalin matasan. Inda akan yi tallar wasu ababan da za su maye guraben miyagun ƙwayoyin da aka haramta sayarwa ko kuma shansu, wanda kan ja hankalinsu.

Wolfgan Götz na cibiyar bincike da yaƙi da miyagun ƙwayoyin yayi tsokaci.

Wolfgang Götz
Wolfgang GötzHoto: picture-alliance/ ZB

"Wuraren da akasarin matasa ke fita domin shaƙatawa ya haɗar da shan ababan da za su sa su maye, wanda a ganinsu wannan ba wani abu ne daban ba, hakan daidai yake. A yawancin lokuta a nan ne akan sha giya da miyagun ƙwayoyi"

Wani abun ban tsoro kuma shine ɗabi'ar sanya waɗannan sinadaran mayen a cikin ababan sha da ake samu a wuraren shaƙatawa da matasan kan ziyarta. Mechthild Dykmans ita ce jami'ar yaƙi da miyagun ƙwayoyi a tarayyar Jamus.

"Babbar matsalar irin waɗannan ƙwayoyi shine, suna ɗaukar lokaci mai tsawo kafin illolinsu su bayyana. Saboda masu shan ƙwayoyin basu san irin illolinsu ba, sukan ɗauki ƙwaya ɗaya su haɗiye, kana su ƙara haɗiye wani bayan rabin awa, idan har basu ji yadda suke so ba. Wanda hakan kan jagoranci lahani ga lafiyar mutum"

Abun da yake zahiri a tarayyar Jamus da nahiyar Turai baki ɗaya dai shi ne, nan bada jimawa ba waɗannan ƙwayoyi masu sa maye za su haifar da illoli fiye da na hodar Iblis da dangoginta. Saboda su na da araha kuma a wuraren yin magunguna ake sarrafa su, ba a gonaki ba. Majalisar Ɗunkin Duniya ta yi nuni da cewa, a yanzu haka ta waɗannan Ƙwayoyin maye ne, miyagun ƙungiyoyin ɓata gari na Mafiya ke cin karensu babu babbaka.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar

Edita : Mohammad Nasiru Awal