1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhi: Makonni hudu gabanin zaben majalisar dokokin Jamus

August 30, 2021

Tsawon lokaci ya kasance tamkar babu wanda zai gaji shugabar gwamnatin Jamus in ba Armin Laschet ba. Sai dai a yanzu jam'iyyarsa ta CDU ka iya tsintar kanta a bangaren adawa bayan zaben ranar 26 ga watan Satumba.

https://p.dw.com/p/3zhjp
Kombild Kanzlerkandidaten Triell | Laschet, Baerbock und Scholz

Felix Steiner ya fara sharhin nasa ne yana mai cewa: Kawo yanzu dai, gangamin yakin neman zaben Jamus ya kasance tamkar rudu. A hannu guda za a iya cewa ya gunduri mutane fiye da tsammani, muhawara tsakanin 'yan takara babu karsashi. Zai ma yi matukar wahala ka samu wani abu mai ma'ana cikin tsarin siyasar. Amma a hannu guda idan aka yi la'akari da yadda abubuwa ke wakana a yanzu, ana iya cewa sakamakon zaben ka iya bayar da mamaki fiye da kowanne lokaci. A yanzu babu tabbacin waye zai gaji Angela Merkel ko kuma su waye za su kafa sabuwar gwamnati.

Abin da ya sanya zaben yafi daukar hankali ma shi ne, shugabar gwamnati ba za ta sake tsayawa takara ba. Karon farko a tarihin Jamus. Sai dai hakan bai kasance babban dalilin da ya sanya zaben ya zama mai rabo ka samu ba. Felix Steiner ya ce wannan ya tuna min da zaben shugaban kasar Amirka da aka gudanar a bara, inda wasu masu zaben ba su da gwani cikin 'yan takara. Za a iya cewa zaben na Jamus na daukar wannan hanya.

Farin jinin hadakar Armin Laschet dan takarar jam'iyyar Christian Democratic Union (CDU) da abokiyar tagwaitakarta ta Bavariya wato Christian Social Union (CSU) da kuma Annalena Baerbock ta jam'iyyar The Greens masu rajin kare muhalli, ya ragu a kuri'ar jin ra'ayin jama'a a makonnin baya-bayan nan. Yayin da ministan kudi kana dan takarar jam'iyyar Social Democrats (SPD) Olaf Scholz ya bayar da mamaki. A baya dai ana ganin babu inda za shi, sai dai a yanzu farin jinin nasa ya kere na takwarorinsa. Rabon da jam'iyyar SPD ta samu irin wannan goyon baya fiye da takawarorinta na CDU da CSU, tsawon shekaru 15.

Ko da yake la'akari da cewa duka wadannan jam'iyyu uku sakamakon jin ra'ayin jama'ar da suka samu bai wuce kaso 20 cikin 100 ba, za a iya cewa an kusa kawo karshen mulkin hadaka na jam'iyyu biyu a Jamus. Hakan na nufin abubuwa ka iya shiga cikin rudani. Akwai hasashen yin hadakar jam'iyyu uku zuwa hudu wato CDU da CSU da SPD da kuma The Greens. Ko kuma CDU da CSU da kuma Free Democrats (FDP), ko SPD da FDP da kuma The Greens ko kuma CDU da CSU da FDP da kuma The Greens. Duka wadannan hadaka, ba lallai su kawo natija mai kyau ba.

Felix Steiner Editan tashar DW
Felix Steiner Editan tashar DW

Ba lallai ne a iya jure tataburzar da aka yi a kokarin kafa gwamnatin hadaka shekaru hudun da suka gabata ba, inda jam'iyyun CDU da CSU da The Greens da kuma FDP suka kwashe tsawon makonni suna tattaunawa ba tare da sun cimma matsayar kafa gwamnatin hadakar ba. Felix Steiner ya ce: a karon farko ina tantamar watsi da ra'ayoyin wasu da ke cewa jawabin Merkel na sabuwar shekara da ta yi a 2020, ba shi ne na farko ba. Hakan ka iya zama tilas. In har zuwa lokacin babu gwamnati ko shugabar gwamnati, tilas Merkel ta ci gaba da zama a matsayin shugabar gwamnatin rikon kwarya.

Jamusawa ka iya ci gaba da harkokinsu. Kasar za ta ci gaba da gudana tsawon wasu watanni. Za a ci gaba da karbar haraji, jami'an 'yan sanda da kotuna da makarantu da jami'o'i za su ci gaba da aiki kamar yadda suka saba. Za a ci gaba da biyan ma'aikata da 'yan fensho. Sai dai hakan ka iya yin illa ga kungiyar Tarayyar Turai, kungiyar da ke zaman maras katabus idan babu Jamus. Duk da yiwuwar tafiyar hawainiya wajen kafa gwamnatin hadaka bayan zabe, sabuwar gwamnatin ka iya zama dagogwarago.

Tilas sabo ko sabuwar shugabar gwamnati, ta tabbatar da cewa ba a samu kishin-kishin din rikicin cikin gida a gwamnatin hadakar ba, yayin da yake ko take fuskantar kalubalen hulda da kuma siyasar kasa da kasa. Koma dai mai ake ciki shugaban Rasha Vladimir Putin da na Chaina Xi Jinping da kuma na Amirka Joe Biden za su sanya idanu, tare da bibiyar al'amura kafa da kafa domin ganin ko za su samu kankanuwar kafar rashin tabbas a gwamnatin da za su yi amfani da ita.