1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhi: Gazawar Trump a ganawa da Putin

July 17, 2018

Shugaban Amirka Donald Trump ya nuna gagarumin rauni a lokacin ganawa da takwaransa na Rasha Vladmir Putin a birnin Helsinki, lamarin da ke zama babban kuskure, a cewar Bernd Riegert wakilin DW a sharhin da ya rubuta.

https://p.dw.com/p/31az1
Finnland Helsinki PK Treffen Trump Putin
Hoto: picture-alliance/Zumapress

Donald Trump zai iya kasancewa shugaba na gari ga Rasha, amma ba ga Amirka da sauran duniya ba. Ana iya tabbatar da wannan matsayi karkashin sakon tweet da Trump ya wallafa kuma ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta sake yayatawa. Shugaban na Amirka ya zargi kasarsa da haddasa mummunar dangantaka da Rasha. Wannan abin kunya ne saboda bai taba faruwa ba a tarihin kasar Amirka. Bayan da ya gana da Shugaba Vladimiri Putin, Donald Trump ya jaddada wannan matsayi, lamarin da ya sa shi tozarta kansa.

Ba a taba samun shugaban kasa me kwance wa kasarsa mazagi a kasuwa kamar wannan ba. Tambaya a nan ita ce har yaushe 'yan jam'iyyar Republican, da magoya bayan Trump za su ci gaba da amincewa da wannan kaskanci da yake nunawa? Shugaban na Amirka ya saba furta kalaman da ke cin karo da juna: Wani lokacin yana cewa kungiyar tsaro ta NATO tana zama karfen kafa ga Amirka, wani lokacin kuma ya nuna mata kauna. Wani lokaci kuma ya dora wannan karan tsanar kan Sin, wasu lokutan kuma ya sanya EU da Sin a layi guda.

A game da Birtaniya kuwa, Trump na nuna cewa ba ta katabus a gaban EU dangane da yarjejeniyar raba gari ta Brexit, wani lokaci kuma ya bayyana firaministar kasar wato Theresa May a matsayin abokiyar hulda ta kut-da-kut. Bayan haka ya nunar cewa Jamus ta kasance karen farautar Putin, amma kuma yana daukar shugaban na Rasha a matsayin abokin tafiya.

Riegert Bernd Kommentarbild App
Riegert Bernd wakilin DW da ya rubuta wannan sharhi

Wannan kwan-gaba-kwan-baya da hamshakin attajiri da ya taba shirye-shirye a talabijin kafin ya zama shugaban kasa ke yi ba abu ne da za a laminta ba. A fili yake cewa Trump bai shirya wa ganawar ba idan aka kwatanta da Shugaba Putin na Rasha. A duk lokacin da Trump ya yi rangadi kasashen waje don bayyana matsayinsa, yana hada ministocinsa da gagarumin aiki na bambance dan duma da kabewa a kan kalaman da ya furta. Wai shin har yaushe za su ci gaba da gyara katobarar da yake tafkawa?

Ana ganin cewa wasan kwaikwayo da Trump ya yi a Helsinki ya zame wa shugaba Putin na Rasha gobarar Titi. Ba abin da ya yi, illa sauraron yadda Donald Trump ke caccakar tsarin da ake amfani da shi a duniya. Ko da a makon da ya wuce sai da ya soki karancin gudunmawar da kasashen Turai ke bai wa kungiyar tsaro ta NATO, sannan ya soki Ingila kuma ya bayyana Kungiyar Tarayya Turai a matsayin abokiyar gaba, lamarin da ya dadada ran Vladimir Putin. Da ma zargin da aka yi wa Putin da Rasha na yin shisshigi a zaben Amirka bai yi tasiri ba. Wai shin Putin ya yi kokarin yin tasiri a zaben na Amirka a shekara ta 2016?  Wai shi ya taimaka wa Trump lashe wannan zabe, ko kuma yana da shaida da ke nuna rawar da bangaren Trump ya taka? Idan aka yi la'akari da abin da ke faruwa, za a ga cewa da walakin, saboda wani ladabi da biyayya da yake nuna wa Rasha.

Wannan shi ne dalilin da ya sa shugaban na Amirka ya gana da tsohon babban jami'in leken asirin a Helsinki. Fannin da shugabannin biyu suka yi kama da juna a kai shi ne rashin damuwa da gaskiya. Putin ya bayyana a fili cewa bai damu a amince da shi ba, amma ya fi raja'a kan manufofin da yake so ya aiwatar. Hakika abu ne mai kyau idan shugabannin biyu suna magana da junansu. Amma kuma hargowar ta Trump na hannun riga da abin da duniya ke bukata. Shugaba Trump ya yi nasarar rike mukami mafi girma, amma kuma ya watsa wa talakawansa kasa a ido.