1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhi kan yaki da Boko Haram

Thomas MöschApril 30, 2015

Sojojin Najeriya bayyana samun nasara a yakin da suke da yan ta'adda inda suka fara kwato matan da aka sace

https://p.dw.com/p/1FISJ
Nigeria Armee rettet Mädchen Symbolbild
Hoto: picture-alliance/dpa/H. Ikechukwu

A wannan sharhi da Thomas Mösch shugaban sashin Hausa na DW ya rubuta yake cewa, ta yiwu hakan nan nuna alamar kawo karshen kungiyar Boko Haram, idan dai bawai da wata manufa sojojin suka yi hakan ba.

Abun na da yuwar hakanli ya yarda ace wai shekaru shida sojojin Najeriya na yaki da kungiyar, amma ace wadannan 'yan ta'adda suke kwadayin zubar da jini, ace sojojin na neman ganin bayansu. Kungiyar Boko Haram, ance tana fagen daga da sojojin Najeriya, Nijar, Kamaru da Chadi. To amma fa rahoton nasarar da sojan Najeriya suka bayar, dole a karbeshi da ayoyin tambaya. Domin kuwa sau da dama sun sha shelar yin nasara kan Boko Haram ko kuma kwato mutane da aka sace, amma daga baya zancen ya zama kanzon kurege.

Don haka yanzu sai mu jira muga labarin da zai fito a kwanaki da ke tafe. A nanne za mu iya tabbatar ko an samu nasarar kwato mata da 'yan mata masu yawa. Wato shin ko da gaske matan sace su aka yi, kana shin akwai 'yan matan makarantar Chibok a ciki, ko kuma mata da yaran kungiyar 'yan ta'addanne. Kuma za a jira a gani ko sojan Najeriya za su dore da rike wuraren da suka kwato.

Al'amuran da suke faruwa a 'yan kwanakinnan na tattabar da cewa, Boko Haram, kungiyace da aka kirkira a cikin gida bisa manufofin siyasa. Al'amura biyau da suka faru za su iya fayyace dalilan da suka sa kungiyar yin nasara a shekarun baya.

Na farko dai sojan Najeriya da shugabannin rundunoni dake Abuja, kana da 'yan siyasa sun gaza daukar mataki bisa munin da kashe-kashen da aka yi wa jama'ar yankin arewa masu-gabashin kasarsu. Biliyoyin kudin da ya dace a baiwa sojojin an bi da su wata hanya ta daban, inda aka sai da rayukan kananan sojoji da dubban talakawa da suka mutu, suka jikkata ko suka rasa gidajensu.

Har sai lokacin da 'yan siyasa da shugabannin sojojin suka ga ne kurensu cewa, gazawar kawar da Boko Haram zai yi sanadin su kasa cin zabe.

Na biyu shi ne, karyewar Boko Haram cikin gaggawa, 'yan ta'addan da in banda 'yan kwanaki ake matukar tsoronsu. Hakan na nufin wadanda ke samar mata tallafi da makamai suna bacewa. Kungiyar na bukatar wannan tallafin fiye da bankunan da suke fasawa da kudin fansa da suke samu wajen mutanen da ake sacewa.

Kawo yanzu babu wata shaidair cewa Boko Haram na samun agajin kudi daga wasu kungiyoyin kasashen waje, hakan na nuna kungiyar na samun tallafinta ne daga cikin kasar. Akwai kuwa alakar bullar kungiyar Boko Haram da lashe zaben shugaba Jonathan a shekaru hudu da suka gabata.

Ba za a ce a hukumomi sunki yakar Boko Haram a baya bisa wata manufa ba. Yanzu dai zabe ya nuna an kawar da Jonathan daga mulki, kuma kungiyar Boko Haram sannu a hankali na dushewa. shin za ace wannan katari ne kawai?.

Kawo yanzu dai babu abin da ke alakanta zababben shugaba Muhammadu Buhari da masu tallafawa Boko Haram. Kai hasalima yana matukar nisanta kansa daga arewa da suka wawuri dukiyar kasa. Yanzu ko Buhari zai iya bankado hanyoyin da Boko Haram ke samun kudinta?, Hakan dai abu ne dake da shakku. Abinda ka iya faruwa shi ne, masu goyon Boko Haram su janye goyon bayan da suke baiwa kungiyar, sai su bar kungiyar ta koma 'yan fashi da makami, kamar dai yadda yake faruwa a sauran sassan kasar, idan hakan ma ta samu.

Deutsche Welle Afrika Haussa Thomas Mösch
Thomas Mösch, shugaban sashin Hausa na DWHoto: DW