1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhin jaridun Jamus kan nahiyar Afirka

Mohammad Nasiru Awal
September 29, 2017

A wannan makon jaridun sun duba batun kamun kifi a wasu kasashen Afirka ba bisa ka'ida ba wanda ake dangantawa da wasu kasashen Turai sannan sun duba batun nan na makwafin kyautar Nobel da a bana wata 'yar kasar Habasha.

https://p.dw.com/p/2kypH
Karte Afrika Übersicht
Batutuwa da dama da suka wakana a Afirka sun dau hankalin jaridun Jamus na wannan makonHoto: DW
Geisternetze
Ana zargin wasu kasashen Turai da yin kamun kifi a Afirka ba bisa ka'ida baHoto: picture-alliance/Woodfall Wild Images/Photoshot/I. Everson

Bari mu fara da sharhin da jaridar Süddeutsche Zeitung ta rubuta wadda a wani labari mai taken "Sata a Teku" ta mayar da hankali kan sana'ar kamun kifi a gabar tekun yammacin Afirka inda ta ke cewa manyan kamfanonin kamun kifi na kasa da kasa na sha'awar yin su a tekun Atlantika a bangaren yammacin Afirka, inda aikin da suka kwashe tsawon shekaru su na yi ya rage yawan kifaye a yankin. Jaridar ta ce wani nazarin da aka yi kwanan nan ya gano cewa kasashen Tarayyar Turai na da hannu dumu-dumu a aikin kamun kifin ta barauniyar hanya duk kuwa da kashedin da aka yi wa kasashen kungiyar kan yin hakan.

Westafrika CFA-Franc BEAC
Ana cigaba da muhawarar kan alfanu ko rashinsa na ci gaba da amfani da takardun kudin CFA a Afirka.Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Ita kuwa jaridar Neue Zürcher Zeitung tsokaci ta yi kan mahawarar da ake yi kan alfanu ko rashinsa na ci gaba da amfani da tsarin takardun kudin CFA a Afirka. Ta ce kasashe Afirka 14 masu yawan al'umma miliyan 155 da suka taba kasancewa karkashin mulkin mallakar kasar Faransa. Akwai takardun kudi biyu wato CFA ta tsakiyar Afirka da kasashe irinsu Jamhuriyar Demokardiyyar Kwango da Chadi da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ke amfani da ita. Akwai kuma CFA ta yammacin Afirka da kasashen Senegal da Cote d'Ivoire da Mali da kuma Nijar ke amfani da ita. A da an alakanta kudin da CFA-Franc amma yanzu da kudin Euro, lamarin kuma da ke shafan darajarsa amma har yanzu Faransa ce ke da cikakken iko a kan CFA din.

Äthiopien Gewinnerin des alternativen Nobelpreises, Yetnebersh Nigussie
Yetnebersh Nigussie 'yar kasar Habasha da ke kare hakkin nakasassu ta lashe lambar yabo makwafin ta NobelHoto: Studio Casagrande

Ita kuwa jaridar Neues Deutschland  ta buga labari ne kan makwafin kyautar Nobel da a bana wata 'yar kasar Habasha da ke fafatukar kare hakkin dan Adam da kuma kare muhalli ta kasance cikin mutane hudu da suka samu kyautar. Jaridar ta ce matashiyar lauya kana makauniya 'yar kasar Habasha da ke gwagwarmayar kare nakasassu Yetnebersh Nigussie ta na cikin mutane hudu da suka samu lambar kyauta makwafin ta Nobel ta zaman lafiya. Nigussie ta samu nasarori duk da irin rashin fahimta da wasu ke da ita bisa nakasa a kasashe masu tasowa na Afirka kamar Habasha.