1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nahiyar Afirka a jaridun Jamus

Mohammad Nasiru Awal LMJ
May 17, 2019

Halin da ake ciki a kasar Sudan da zaben kasar Afirka ta Kudu da kuma rikicin kasar Kamaru, sun dauki hankulan jaridun Jamus a wannan makon.

https://p.dw.com/p/3Ieow
Sudan Protest
Zanga-zanga a Sudan ta sauke Al-Bashir tare da tilasta kafa gwamnatin riko.Hoto: Getty Images/AFP/M. el-Shahed

Jaridar Neues Deutschand ta yi sharhinta kan halin da ake ciki a kasar Sudan tana mai cewa: Watanni biyar na jerin zanga-zanga da asarar daruruwan rayukan mutane da wasu bila adadin da aka tsare, an kifar da gwamnatin shugaban kasa Omar Hassan Al-Bashir an kafa majalisar mulkin soja. Bayan wadannan fadi tashin, an hango karshensa. A ranar Laraba majalisar mulkin soja ta wucin gadi da wakilan masu zanga-zanga, sun amince da wata yarjejeniya da ke da nufin kafa gwamnatin riko ta tsawon shekaru uku, wadda za ta kai kasar ga tsarin mulkin dimukuradiyya. Jaridar ta ce hatta kungiyoyin 'yan tawaye sun sanar da shirin tsagaita wuta. Gwamnatin za ta kunshi wakilai daga dukkan bangarorin da ke da ruwa da tsaki a kasar.

Dama ta karshe:


Wannan shi ne taken sharhin da jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta rubuta dangane da nasara da jam'iyyar ANC da ke mulki a kasar Afirka ta Kudu ta samu a zaben majalisar dokokin kasar na makon da ya gabata. Jaridar ta ce a dole shugaban ANC kuma shugaban kasa Cyril Ramaphosa ya karbi sakamakon zaben na kashi 57 cikin 100, da ke zama irinsa mafi muni da jam'iyyar ta taba samu tun bayan kawo karshen mulkin nuna wariyar launin fata shekaru 25 da suka gabata. Shugaban ya yi alkawarin tsabtace jam'iyyarsa da ke fama da rarrabuwar kai. Ana kuma zargin wasu kusoshinta da cin hanci da rashawa da ma kaucewa daga ainihin manufofinta na tafiyar da mulkin gaskiya da adalci. Yanzu dai al'ummar kasar ta ba wa jam'iyyar sabuwar damar yin sabon wa'adin mulki da fatan za ta share wa 'yan kasar hawaye.

Südafrika Präsident Cyril Ramaphosa
Shugaba Cyril Ramaphosa na Afirka ta KuduHoto: AFP/M. Spatari

Halin da ake ciki a Kamaru ya kai wani mizani na bala'i


Jaridar Neue Zürcher Zeitung ta ce a farkon mako Majalisar Dinkin Duniya ta yi zama na musamman kan halin da ake ciki a yankin masu amfani da turancin Inglishi na Kamaru. Jaridar ta ce mawuyacin halin da ake ciki a Kamaru ba ya fitowa bainar jama'a. A cikin watanni 20 da suka gabata, rikicin yankin yammacin kasar ya yi sanadin rayukan mutane 1850, an tilasta wa fiye da rabin miliyan tserewa, inda wasu dubun dubata suka gudu zuwa kasashen ketare, musamman makwabciyar kasa Najeriya. Alkalumman da Majalisar Dinkin Duniyar ta bayar sun ce 'yan Kamaru miliyan hudu ne rikicin ya shafa, miliyan guda da rabi daga cikinsu na fama da matsalar karancin abinci sakamakon rikicin. A nasa bangaren shugaban kasa Paul Biya mai shekaru 86 wanda kuma tun a 1982 yake kan karagar mulki, ya kasa magance matsalar musamman ma ta korafin da yankin na masu magana da Ingilishin ke yi cewa an mayar da su saniyar ware a harkokin kasar.

Kamerun Zentralafrikanische Republik Flüchtlinge in Kousseri
Rikicin Kamaru ya tilasta wa mutane yin hijiraHoto: AP