1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shariár Charles Tyalor a birnin Hague

March 31, 2006
https://p.dw.com/p/Bv3e

Kotun kasa da kasa ta majalisar dinkin duniya dake shariár laifukan yaki ta bukaci maida shariár tsohon shugaban kasar Liberia Charles Taylor daga Saliyo zuwa birnin Hague a kasar Netherlands saboda matakan tsaro.

A ranar Larabar da ta gabata ce aka tasa keyar Charles Taylor sanye da ankwa a hannun sa zuwa kasar Saliyo domin amsa tuhuma a kan laifukan yaki. Charles Taylor zai kasance tsohon shugaba na farko a Afrika da zai gurfana a gaban kotun kasa da kasa. Babban mai shariár Justice A Raja N. Fernando ya baiyana fargabar cewa magoya bayan Charles Taylor na iya tada yamusti a lokacin zaman shariár. Maáikatar harkokin wajen kasar Netherland da kuma kotun ta kasa da kasa na nazarin bukatar domin bada sahalewa. A waje guda kuma shugabar kasar Liberia Ellen Johson Sirleaf ta baiyana cewa dangi da yan uwan Charles Taylor da kuma masu yi masa hidima wadanda har yanzu suke zaune a Nigeria na iya dawo wa gida ba tare da wata fargaba ba, domin ba zaá tuhume su da wani laifi ba.