1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shariar El-Motassadeq a Hamburg

January 6, 2007
https://p.dw.com/p/BuVN

Bisa dukkan alamu ,aranar litinin din nan ne zaa zartar da hukunci,kann dan kasar Morokon nan da ake shariarsa anan jamus dangane da hannu a harin 11 ga watan Satumba ,wa Amurka.Kotun dake sauraron shariarsa a birnin Hamburg,ta fara sauraron zagaye na ukun shariar,Mounir el-Motassadeq,mutumin farko dake zaman yari adangane da hare haren na Amurka.Bisa dukkan alamu zaa dada fadada waadin zaman gidan yarin da yakeyi daga shekaru 7 zuwa 15.A watan Nuwamnban daya gabata nedai aka samu El-Motassadeq da laifin kasancewa,dan wata kungiyar tarzoma,da kuma hadin baki da wadanda suka shiga jiragen da suka kai hare haren na 11 ga watan Satumba.