1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shari'ar kisan kiyashin Ruwanda a Paris

Yusuf BalaMay 10, 2016

Mutane 2000 'yan kabilar Tutsis ne suka halaka bayan da suka nemi mafaka a majami'u a garin Kabarondo a lokacin yakin basasa a kasar Ruwanda.

https://p.dw.com/p/1IlHi
Ruanda Präsident Paul Kagame
Shugaba Paul KagameHoto: picture-alliance/AP Photo/S. Senne

Wasu tsofaffin magadan gari biyu a kasar Ruwanda sun gurfana a gaban kuliya a birnin Paris bisa zargin hannunsu a harzuka magoya baya, abin da ya yi sanadi na kisan kiyashin kabilar Tutsis a ranakun farko na yakin da kasar ta fada a shekarar 1994.

Tite Barahirwa dan shekaru 64 da Octavien Ngenzi dan shekaru 58, ana zarginsu da laifukan aikata kisan kiyashi da laifin yaki da cin zarafin bil Adama, bayan kisan mutane 2000 'yan kabilar ta Tutsis da suka nema mafaka a majami'u a garin Kabarondo. Dukkanin mutanen biyu dai idan har aka samesu da laifi za su iya share lokutan rayuwarsu a gidan kaso.

Rikicin da kasar ta Ruwanda ta fada dai a shekarar1994 ya yi sanadi na rayukan mutane 800,000 mafi yawa 'yan Tutsis da 'yan kabilar Hutu suka halaka.