1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shari´ar membobin ƙungiyar yan uwa musulmi na Masar

August 4, 2007
https://p.dw.com/p/BuEl

Hukumar kare haƙƙoƙin bani adama ta ƙasa da ƙasa, wato Amnesty International, ta yi kira ga shugaban ƙasar Masar Hosni Mubarack ya yi adalci ga shari´ar da za a fara gobe, ta wawu mutane 40 yan ƙungiyar yan uwa musulmi na wannan ƙasa.

Tun watan desember na shekara ta 2006, gwamnatin Masar ta capke wannan mutane, da ta ke zargi da buga kuɗin jabbu da kuma ɗaurewa yan ta´ada gindi.

An gurfanar da mutanen gaba kotun soja, wadda a cewar ƙungiyoyin kare haƙƙoƙin jama´a ba ta da cikkaken yanci, sannan idan ta yanke hukunci, babu damar ɗaukkaka ƙara.

A cikin wasiƙar da ta aika ,Amnesty ta bukaci hukumomin Masar su ba ƙungiyoyin masu zaman kansu damar sa ido ga shari´ar.

Ƙungiyar yan uwa musulmi ta ƙasar Masar, haramttata ga gwamnati, to amma a halin yanzu ta na riƙe da kashi 1 bisa 5, na yawan yan majalisar dokokin ƙasar.