1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shari'ar mutumin da ake zargi da hannu a harin Madalla

April 19, 2013

Babbar kotun tarayya da ke birnin Abujan Najeriya, ta fara zaman sauraren shari'ar Kabiru Sokoto da ake tuhumai da kulla makarkashiyar kai hare hare a Najeriya.

https://p.dw.com/p/18Jf5
Hoto: Picture-Alliance/dpa

An dai gabatar da Kabiru Umad da aka fi sani da Kabiru Sokoton ne a babbar kotun da ke Abuja inda aka karanta masa laifuffukan da ake zarginsa da aikatawa da suka hada da kulla makarkashiyar kai hare-hare da suka hada da harin bom a cocin St. Theresa da ke unguwar Madalla a gefen Abuja, harin da ya yi dalilin mutuwar mutane 44 da jikata 75 a ranar Krismatin 2011.

Nan take dai Kabiru Sokoto ya musanta dukkanin laifuffukan da gwamnatin Najeriyar ke tuhumarsa da aikatawa, tare ma da cewa shi ba dan kungiyar Ahlu Sunnah Li Da'awati Waljihad ba ne. Barrister Adamu Ibrahim shi ne jagoran lauyoyin da ke kare shi a shari'ar ya bayyana cewa ba kawai Kabiru Sokoto ya musanta lafin da ake zarginsa ba ne, akwai ma muhimmin batu a kan wannan sharia.

‘"Ba ma ya musanta ba kawai tuhume tuhumen da ita gwamnatin Najeriya ta gabatar a kansa, bai ma nuna cewa shi ne ya aikata wadannan laifuffukan ba, abinda kawai suka ce shi ne wai ya taimaka wa wadansu yara da niyya, da niyya aka ce zai tarwatsa ofishin kwamishinan 'yan sanda a Saokoto, na biyu kuma an ce yana sane da wadanda suka tada bom a cocin St. Theresa Catholic da ke Madalla, kuma bai shada wa jami'an tsaro ga abinda yake sane da shi ba."

Tura wanda ake wa shari'a zuwa gidan yari

To sai dai lauyoyin gwamnatin Najeriya da ke gabatar da kara sun ki cewa uffan a kan wannan shari'a da aka dade ana ja in ja a kanta, da ma ake wa kallon na da sarkakiyar sosai.

Mai shari'a Adeniyi ya ba da umurnin a karbe ikon tsare Kabiru Sokoto daga jami'an hukumar tsaro ta SSS don a kai shi gidan yari, domin a bai wa iyalansa da lauyoyinsa samun damar ganawa da shi a duk lokacin da suka bukata. Kabiru Sokoto dai ya bayyana a kotu ne cikin natsuwa.

Bombenanschlag Nigeria
Hoto: picture-alliance/dpa

Kabiru Sokoton da jerin lauyoyi guda biyar suke kare shi kamar yadda mai shari'a Adeniyi Ademola ya bukata cewar lallai sai a sama masa lauyan da zai kare shi, ya bayyana a kotun sanye da doguwar rigarsa cikin natsuwa a lokacin da aka gudanar da shri'ar, inda jami'an tsaro suka yi wa kotun kawanya tare da daukan tsauraran matakan tsaro a ciki da ma zagayen kotun.

Share fage ga shari'un mutane da ake tsare da su

Ko da yake ana kalon wannan shari'a a matsayin wacce ke share fagen tuhumar mutane da dama da ake tsare da su da irin wadannan laifuffuka ba tare da an kaisu a gaban kotu ba, amma masharhanta na ganin akwai bukatar hanzarta yin hakan domin ci gaba da tarse su ba tare da tuhuma ba ya saba wa dokar kasa da ma 'yancin bani Adama. Malam Hussani Mongunu masanin harkokin tsaro ne a Najeriyar.

Dossierbild 3 Gewalt in Nigeria
Hoto: Reuters

"Yaran nan da suke kai wadannan hare-hare ba mu ce duk abinda suka fada a yarda da su ba, amma wadanda aka kama a gurfanar da su a gaban kotu mana, muna da mutane kusan dubu shida wadanda yunwa da kishirwa na kashe su. Yau babu gida a arewa da cin zarafin jami'an tsaron nan bai shafa ba, yaya za'a yi a shawo kan wannan matsala? Domin 'yan Boko Haram sun mutu da yawa jami'an tsaro sun mutu da yawa talakawa sun mutu."

An dai dauki tsauraran matakan tsaro a lokacin shari'ar inda Alkali Adeniyi ya dage sauraran karar tare da tsayar da ranakun 2 da 6 da kuma 9 ga watan Mayu domin ci gaba da shari'ar ta Kabiru Sokoto abin da ke nuna alamun zai yi shari'ar cikin hanzari domin kaiwa ga yanke hukunci.

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita: Mohammad Nasiru Awal