1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shari´ar tsofan shugaban kasar Iraki Saddam Hussain

December 7, 2005
https://p.dw.com/p/BvHb

A kasar Iraki kotu ta koma sauraran shari´ar tsofan shugaban kasa Saddam Hussein, saidai Saddam ya yi tawaye ga zaman na yau, domin nuna fushin sa a kan tozarcin da ya ce a na yi masa, da kuma rashin adalici , da a cewar sa, kotu ke nunawa.

A zamman jiya, an saurari shaidu 5, a game da zargin da ake yi ma tsofan shugaban kasar ,na hallaka mutane 148 ,a garin Dujail, a shekara ta 1982.

Shugaba Bush na Amurika, ya yabawa yadda shari´ar ke gudana, kazalika Praministan Iraki, Ibrahim Jafari,daya ce bashi da kwakwanto, a game da adalici kotun, a yayin da Saddam Hussein, da alkalan sa ,ke ci gaba da nuna rashin cencentar ta.

Shari´ar na gudana a yiyin da hare haren kunar bakin wake, ke gaba da kara kamari a sassa daban daban na kasa.

A sahiya yau yan takife su ka kai hari ga babban assibitin Kirkiuk, inda su ka hallaka yan sanda 3.

A hannu daya Ayman Alzawahiri na hannun damar Ussama Bin Laden, ya gabatar da jawabi a fafen Video, inda ya tabatar da cewa, Usama na da rai, kuma har yanzu,shi ke jagorancin hare haren da kungiyar Alqa´ida ke kaiwa, a sassa daban daban na dunia.