1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shawo kan matsalar bakin haure a Turai

LateefaOctober 9, 2013

Shugaban Hukumar Tarayyar Turai zai kai ziyara Tsibirin Lampedusa domin ganewa idonsa halin da ake ciki, bayan da wasu bakin haure suka yi hadari a Tsibirin.

https://p.dw.com/p/19wVR
Hoto: Petras Malukas/AFP/Getty Images

Ana sa ran shugaban hukumar kungiyar Hadin KanTurai Jose Manuel Barroso, zai kai ziyarar gani da ido zuwa Tsibirin Lampedusa dake kasar Italiya, biyo bayan hadarin da da wani jirgin ruwan fasinja makare da bakin ya yi a Tsibirin wanda kuma ya yi sanadiyyar mutuwar kimanin bakin hauren da dama.

Ziyarar tasa dai na zuwa ne bayan da ministocin cikin gida na kungiyar suka gana, inda kwamishiniyar harkokin cikingida a kungiyar ta Hadin Kan Turai wato EU Cecilia Malmström, ta bukaci da a fara gudanar da sintiri a gabar Tekun Mediterranean, tare da shan alwashin yin kokari domin ganin ta samu goyon baya wajen samar da karin kudade da kuma kayan aiki, da za a fadada ayyukan sintirin daga Tsibirin Cyprus zuwa kasar Spain, domin rage asarar rayukan da ake yi a yankin.

Masu ceto dai na ci gaba da kokarin gano ragowar barakuzan jirgin da ya ke dauke da 'yan gudun hijira sama da 500 mafi akasarinsu 'yan kasasshen Somaliya da Habasha, bayan da suka yi nasarar ceto mutane 155 da ransu, yayin da kawo yanzu suka gano gawawwaki sama da 270.

Mawllafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu