1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shawo kan matsalar rikicin zaɓe a Najeriya

February 20, 2013

Wata ƙungiya mar rajin kare demokraɗɗiya ta yi wani zaman taro dan tattauna hanyoyin kaucewa rikicin zaɓukan Najeriya a dai-dai lokacin da fagen siyasar ƙasar ke ɗaukar zafi

https://p.dw.com/p/17iDD
Bis 12 Uhr müssen sich alle Wahlberechtigten akkreditieren lassen *** Wer hat das Bild gemacht/Fotograf?: Katrin Gänsler Wann wurde das Bild gemacht?: 26. April 2011 Wo wurde das Bild aufgenommen?: Jos, Nigeria
Hoto: DW/Gänsler

Shekaru kusan biyu da sake zagayowar sabbabin zaɓuka a cikin tarrayar Najeriya hankali ya fara karkata ga tashe-tashen hankulan dake zaman ruwan dare ga batun zaɓuka da siyasa a kasar

Tuni dai dattawa suka fara ƙorafin yiwuwa ta gazawa dama nuna alamun rushewar ta a tarrayar Najeriya da ta sha da ƙyar da gumin goshi a zaɓukan tarrayar na 2011 yanzu haka kuma ke shirin fuskantar wasu zaɓukan cikin yanayi na rashin tabbas.

Ga dai matsala ta rashin tsaro, ga kuma mummunan talauci a tsakanin al'ummarta sannan kuma an yi nisa a tsakanin shugabanni da talakawan da suke mulka amma kuma an tasamma shekara ta 2015 daga dukkan alamu a cikin ɗarɗar da faɗuwar gaba.

A cewar mahalarta wani taron wuni guda kan rashin ɗa'a da tashin hankali na siyasar dake zaman ruwan dare a ƙasar da kuma yanzu haka ke zama barazana a tsakanin sarki dama talakan cikin kasar ta Nigeria.

Taron ƙarƙashin jagorancin cibiyar Konrad Adenauer Stiftung mai cibiyar ta a tarrayar Jamus dai na can na nazarin rawa ta 'yan siyasa da jami'an tsaro da ma mallamai irin na addini da sarauta sannan da su kansu matasa a cikin rikicin siyasar da ya kai ga asarar rayuka kusan dubu 2000 ashekaru biyun da suka gabata.

Hanyoyin Kaucewa rikicin siyasa a Najeriya

Abun da kuma a cewar Hildergard Behrendt –Kigoza ya tilasta cibiyar neman mafita da duban hanyar kaucewa sake bulla lamarin.

Nigeria Unruhen Wahlen Jugendliche epa02694632 A photograph made available 19 April 2011 shows Nigerian youths riot near a burning barricade in Kaduna in northern Nigeria, 18 April 2011. Riots broke out across the north of Nigeria as the results of presidential elections indicated incumbent president Goodluck Jonathan the winner. Homes of supporters of president Jonathan were attacked in cities across the north and thousands have been displaced. President Jonathan has appealed for an end to the violence and imposed a curfew. EPA/STR +++(c) dpa - Bildfunk+++
Hoto: picture-alliance/dpa

"Magana daga tarihi da cibiyar mu ta jamus ina mutakar farin ciki na kasancewa tare daku domin taimaka wa kasar ku ta tarrayar Nigeria kaiwa ga samar da tsarin siyasar da ke cike da yanci a cikinsa. Ina fatan ganin taka rawa wajen tattaunawa da nufin samar da alummar da babu tashin hankali a cikin ta".

Tattaunawar kuma da ta haifar da banbancin ra'ayi a tsakanin bangarori daban daban na kasar ta Nigeria.

Madam Sarah Jibril dai itace ke baiwa shugaban Najeriyar shawara ga batun da'a da sanin ya kamata, kuma a cewar ta mafita na zaman matsin lamba ga shugabanni na siyasa a cikin tarrayar Nigeria.

To sai dai kuma in har a tunanin Jibril din dake zaman yar jamiyyar PDP tashe tashen na zaman alama ta gazawa a bangaren shugabannin addini da kabila a idanun Eng buba Galadima dake zaman jigo a cikin sabuwar jamiyyar APC dai rikicin zai zamo tarihi ne kawai in har hukumar zabe da alkalan kasar ta Nigeria sun sauya.

Tuni dai fagen siyasar kasar ya fara ɗaukar zafi a tsakanin sassa daban-daban dake tunanin mulkar kasar ta Nigeria cikin shekaru biyu masu zuwa

To sai dai kuma duk wani tashin hankali a tunanin Abubakar ɗan Asabe Umar dake zaman masani na cigaban alumma zai bata ne kawai in har matasa sun kwanda da aiki da sanoin yi a tsakaninsu.

Abun jira a gani dai na zaman mafita ga tarrayar Nigeria da ke cika shekaru dari a matsayin kasa guda amma a cikin hali na dardar da rashin tabbas.

Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Zainab Mohammed Abubakar