1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekara guda bayan juyin mulki a Mali

March 21, 2013

A bara ne dai Mali ta tsinci kanta cikin juyin mulkin sojoji, batu da yanzu ya jagoranci kutsawar sojojin ketare zuwa cikin kasar domin samar da zaman lafiya.

https://p.dw.com/p/182F7
Titel: DW_ Tuareg_Burkina-Faso4: Schlagworte: Tuareg, Mali, Burkina Faso, Flüchtlinge, Befreiungsbewegung von Azawad Wer hat das Bild gemacht/Fotograf?: Katrin Gänsler Wann wurde das Bild gemacht?: 12. März 2013 Wo wurde das Bild aufgenommen?: Djibo, Burkina Faso
Hoto: Katrin Gänsler

A ranar 21 ga watan maris na shekara ta 2012 nedai cikin sao'i kalilan sojoji suka kai farmaki kan fadar shugaban Mali dake birnin Bamako. Da hakane jami'in soji Amadou Sanogo ya samu kansa a matsayin mai jan akalar mulkin kasar, bayan hanbare shugaban Malin na wancan lokaci Amadou Toumani Toure. Ga al'ummar kasar dai wannan ya kasance mafarin fadawarsu cikin hali na rashin sanin makoma. Masu tsananin kishin addinin Islama da kungiyoyin 'yan tawayen Abzinawa, sun yi amfani da rikicin juyin mulkin dama rigingimu na siyasar da birnin Bamakon ya samu kansa ciki, wajen kame madafan ikon yankin araewavcin kasar. Dubban daruruwan mazauna yankin arewacin ne suka tsere zuwa kasashen dake makwabta da birnin Bamako, sakamakon rigingimun da suka biyo baya.

Shekara guda bayan wadannan rigingimu, mafi yawa daga cikin wadanda suka kaurace daga matsugunnensu na muradin komawa gida, kamar Ismael Maiga wanda ya kasance a birnin Bamako da barkewar wannan rikici, yanzu kuma gashi nan a tashar manyan motoci yana kokarin sayen tikitin komawa yankin arewaci.

Mali's junta leader Amadou Haya Sanogo poses for a picture after agreeing to hand over power to the president of the National Assembly at his office at a military base in Kati in this April 7, 2012 file photo. When former colonial power France sent warplanes and troops to Mali on January 11, 2013 in a historic intervention, it did not just halt a menacing advance on the capital Bamako by Islamist rebels allied to al Qaeda. It also snuffed out what diplomats and local politicians say was a political conspiracy in the capital to oust Mali's interim civilian rulers, an attempted replay of the March 2012 coup that had plunged the Sahel state into turmoil and made it a potential launch pad for attacks on Western interests. To match Insight MALI-RECONSTRUCTION/ REUTERS/Joe Penney (MALI - Tags: POLITICS PROFILE CIVIL UNREST CONFLICT MILITARY)
Jagoran juyin mulki Amadou SanogoHoto: Reuters

"kwarai kuwa, domin kuwa yanzu kowa yana muradin komawa gida".

Shima wannan dan kudun hijira daga arewacin Malin dake layin sayen Tikiti ya amince da hakan.

" A nan mun samu mafaka. Amma anan kudanci bama jin dadi. Ya zamanto dole yanzu mu koma matsugunnenmu na asali. Domin yanzu akwai zaman lafiya".

Tun a farkon watan janairu nedai jiragen yaki masu saukar ungula na sojojoin faransa suka fara kai farmaki akan abunda suka bayyana mabuyar masu tsananin kishin addini dama 'yan tawayen dake rike da yankin arewacin Mali, wanda keda nufin dakatar dasu daga yunkurinsu na isa babban birnin kasar ta Bamako. Tun daga wannan lokaci nedai, aka cimma fatattakar 'yan tawayen daga manyan biranen arewacin kasar. Kazalika runfdunar sojin saman Jamus ta bada goyon bayanta ga wannan shri. Da jiragen sama na daukar kaya guda uku, ta tallafa wajen jigilar sojojin kasasahen ECOWas dake makwabtaka zuwa Mali. Daga lokacin ne aka bar jirgi guda a yancin yammacin afrika, domin taimaka wajen sa mai a jiragen yakin Faransa. Wannan dai na daya daga cikin muhimman tallafin ketare da jamus keyi, acewar lieutenant conel Jörg Bartl na rundunar sojin saman kasar.

Ya ce " saboda sufurin sama da sanya mai a jiragen saman dake yaki, abubuwa ne masu matukar muhimanci ga ayyukan da ake tafiyarwa".

Titel: DW_ Tuareg_Burkina-Faso4: Schlagworte: Tuareg, Mali, Burkina Faso, Flüchtlinge, Befreiungsbewegung von Azawad Wer hat das Bild gemacht/Fotograf?: Katrin Gänsler Wann wurde das Bild gemacht?: 12. März 2013 Wo wurde das Bild aufgenommen?: Djibo, Burkina Faso
Yara a sansanin 'yan gudun hijiraHoto: Katrin Gänsler

Wani abunda keda muhimmanci shine, a bangaren tallafin horarwa na turai, a watan Afrilun wannan shekara ta 2013 ne, Jamus zata fara gudanar da ayyukan horar da dakarun Mali. Ministan tsaron kasar Thomas de Maiziere ya tabbatar da hakan a ziyara daya kai Mali a 'yan kwanakin nan. Jamus zata tura jami'an soji 330 zuwa Mali, wadnad zasu taimaka wajen horar da sojojin Mali, tare da taöllafa musu wajen gina asibitoci a sansanoni.

A birnin na Bamako dai shuga Diocounda Traore na cigaba da kokarin daidaita lamuran siyasa. A watan Afrilun shekakara ta 2012 nedai tsohon kakakin majalisar kasar ya karbi ragamar shugabancin gwamnatin rikon kwarya, bayan cimma yarjejeniya da shugaban kifar da mulki Sanogo. Shugaba Traore dai ya tsayar da watan yuli a matsayin lokacin da za'a gudanatr da zaben 'yan majalisa dana shugaban kasa.

Mawallafiya : Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Mohammad Nasir Awal

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani