1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekara guda da juyin mulki a Gini-Bisau

April 12, 2013

Ranar 12 ga Afirilun 2012 sojoji suka hamɓarrar da zaɓaɓiyar gwamatin farar hula a Gini-Bisau tare da soke zagaye na biyu na zaɓen shugaban ƙasar da ake shirin gudanarwa.

https://p.dw.com/p/18EqG
epa03180815 (FILE) A file photograph showing soldiers at the D'Amura Military Headquarters in Bissau after a military coup d'etat in Bissau, Guinea-Bissau, 01 April 2010. Media reports on 13 April 2012 state that members of the military have taken control of many areas of the capital of Guinea-Bissau and the Presidential Palace of Carlos Gomes Junior has come under attack. EPA/MOUSSA BALDE *** Local Caption *** 00000402100863 +++(c) dpa - Bildfunk+++ pixel
Hoto: picture-alliance/dpa

A ranar 29 ga watan Afirilu na shekara ta 2012 aka tsara gudanar da zagaye na biyu na zaɓen shugaban ƙasar,tsakanin tsohon fira ministan ƙasar Carlos Gomes Junior, da kuma Koumba Yala. To amma sojojin sun kifar da mulkin kuma suka girka gwamnatin wucin gadi tare da bayyana aniyar su na gudanar da wani sabon zaɓe a shekara ta 2013, sai dai har yanzu ƙasar ta na cikin rashin sannin tabbas.

An dai kai ga shirya zaɓuɓɓukan ne na ƙasar ta Guinea Bissau a shekarat ta 2012 bayan mutuwar shugaban ƙasar malan Bacai Sanha a ranar tara ga watan Janeru, wanda ya yi jinya mai tsawo sakamakon rashin lafiyar da ya yi fama da ita. Kuma kamar yadda kudin tsarin mulki na ƙasar ya tanada ya ummarci da a gudanar da zaɓen a cikin kwanaki 90 bayan mutuwar shugaban.

Rashin Tabbas na sake dawo da mulkin dimokaradiyya

A zagaye na farko dai na zaɓen babu ɗan takarar da ya sami kishi 50 na ƙuri'un da aka kaɗa, shi yasa aka shirya yin zagaye na biyu kuma ana ciki shirin yin haka sojoji suka yi juyin muki, kuma suka tsare shugabanin. Carlos Gomes tsohon fira minista na tunawa a lokacin da sojojin ɗauke da man'yan bidingogi suka sallama a gidansa kuma suka tafi da shi. Ya ce: ''Gaba ɗaya suka lallata ginin gidana da harbe harben bindigogi sannan suka kwashi kayan ɗaki, na dauki hoto bidiyo, al'amarin da ya faru.''

P1000675.JPG Titel: Carlos Gomes Junior Schlagworte: Guinea Bissau , Carlos Gomes Junior, Wer hat das Bild gemacht/Fotograf?: João Carlos (DW Korrespondent) Wann wurde das Bild gemacht?: 08.11.2012 Wo wurde das Bild aufgenommen?: Lissabon, Portugal Bildbeschreibung: Pressekonferenz der gestürtzte premie minister aus Guinea Bissau Carlos Gomes Junior in einen Hotel in Lissabon
Carlos Gomes Junior tsohon fira ministaHoto: DW/João Carlos

Ba shakka zaɓen na zagaye na biyu ko da an yi shi ,da to kam tsohon fira minista Carlos Gomes Junior, shi ne ake kyauttata zaton zai sami nasara a gaban Koumba Yala wanda ya samu kishi 23 yayin da Carlos ke da kishi sama da 45. Sannan masu nazari akan al'amura na cewar tsohon fira minista shi ya janyo kansa domin kuwa ya yi barazanar kawarar wasu sojojin da yake zargi da gamin baki da masu fataucin hodar ibilis.

An ɗage sabon zaɓen da aka shirya yi a cikin watan Mayu

Akan ƙaida dai a ƙarshen wannan wata gwamnatin wucin gadi da shugaban riƙo Manuel Serifo Nhamadjo ke jagoranta ya kamata ta kawo ƙarshe, kana kuma a shirya zaɓen shugaban ƙasa a cikin watan Mayu. To amma a lokacin da ya ke yin magana ta gidan talbijan na ƙasar shugaban ya ce ko kaɗan ba zai yiwu ba a shirya zaɓen a cikin watan saboda wasu dalilai na rashin shiri. Fira minista mai ci yanzu ya yi ƙarin bayyani. Ya ce:''Yan ƙasa zasu yi nazarin wani sabon lokaci ko rana da ta dacce domin gudanar da zaɓuɓɓukan bayan mun tattauna da dukanin sauran yan siyasa na ƙasar.''

epa03184134 A soldier disperses a group of demonstrators protesting against the current political situation in Guinea-Bissau, in the country's capital Bissau, 15 April 2012. Political leaders gathered for a third day of talks in Bissau, under direction from military leaders to find a solution to the country's crisis, brought on by soldiers seizing the interim president and prime minister less than 72 hours prior. On 12 April 2012 a group of Guinean military attacked the residence of Prime Minister and presidential candidate, Carlos Gomes Junior, and held various strategic points in the capital of Guinea-Bissau. The events preceded the beginning of the campaign for the second round of the presidential election scheduled for 29 April. EPA/ANDRE KOSTERS
Guinea-Bissau MilitärputschHoto: Reuters

A dai tarihi na ƙasar ta Guinea Bissau wace ke fama da talauci duk kuwa da yadda ta mallaki arzikin ma'addinai, babu wani shugaban ƙasar da ya taɓa kammala wa'adin aikinsa. Shugabannin ukku sojojin suka sauke kafin ƙarshen wa'adi, aka kashe ɗaya kana ɗaya ya mutu cikin aiki da rashin lafiya.

Daga ƙasa za a iya sauraran wannan rahoto

Mawallafi : Abdourahamane Hassane

Edita : Usman Shehu