1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekara kwana inji masu iya magana

October 29, 2013

A tsawon shekaru 50 da kafuwarsa, sashen Hausa na DW ya taka muhimmiyar rawa a fannin yaɗa labarai da sharhuna ga Afirka da ma duniya baki ɗaya.

https://p.dw.com/p/1A7gy
Mitarbeiter des Haussa-Programms in Studio; Copyright: DW
50 Jahre Haussa RedaktionHoto: DW

Shekaru 50 na labarai da sharhuna don Afirka Ta Yamma

Ranar 4 ga watan Nuwamban shekara ta 1963, Deutsche Welle (DW) ta toshe wani ƙaton giɓi a shirye-shiryenta: fara shirye-shiryen rediyo na harshen Hausa ya sanya cikin dare ɗaya mazauna Afirka Ta Yamma suka sami damar sauraren 'yantattun labarai da rahotanni cikin harshensu na asali.

Al'umma mazauna ƙasashen da basu daɗe da samun mulkin kansu ba, sun nuna buƙatar samun amintattun labarai da rahotanni ba tare da ƙarin gishiri ba daga yankunansu da sauran duniya baki ɗaya.

Sashen Hausa na DW tun daga tushe ya sanya burin cimma waɗannan buƙatu na masu saurare, tare da bai wa masu hulɗa da shi damar jin labarai da shirye-shirye amintattu kuma masu nagarta.

A lokaci guda, tushen aikinmu aka ɗora shi kan darajar kare 'yancin ɗan Adam da demokraɗiyya. A daidai lokacin da manyan daulolin duniya suka kasance masu gaba da juna, tashar DW ta yi tsayin-daka a kasancewarta muryar 'yanci da zaman lafiya.

A yau, shirye-shiryen sashen Hausa na DW sun zama abin da a yanzu mutane masu yawa suka dogara da su: suna cike giɓin dake samuwa a kafofin yaɗa labarai na cikin gida, musamman a ƙasashen da ake tauye 'yancin kafofin yaɗa labaran.

Sashen Hausa na DW yana alfahari da kasancewa tushen labarai da rahotanni masu nagarta da aminci, inda za a iya sanin halin da duniya take ciki tare da maida hankali ga nahiyar Afirka.

Shirye-shiryen rediyo na asali yanzu sun canza zuwa ga tuntuɓar juna tsakaninmu da masu sauraro.

A ɓangaren shirye-shiryenmu na Intanet, wato dw.de da kuma a sauran fannoni na cuɗanya, muna samun musaya da tattaunawa sosai tsakaninmu da ku.

Saboda haka ne sashen Hausa na DW ko bayan da ya cika shekaru 50, yana nan sabo kuma mai nagarta kamar yau aka buɗe shi. Muna miƙa godiya matuƙa ga duka abokanmu, saboda wannan nasara da muka samu tare da haɗin kai gaba ɗaya da ku.