1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Shekaru 10 na rashin tabbas bayan kashe Gaddafi

Abdullahi Tanko Bala MA
October 20, 2021

Tun bayan kisan gillar da aka yi wa tsohon shugaban kasar Libya Muammar Gaddafi shekaru goma da suka wuce, har yanzu kasar ba ta fita daga dambarwar rikici ba. Hatta zaben kasa da aka shirya yi a watan Disamba an dage.

https://p.dw.com/p/41vuh
Libyen Führer Muammar al-Gaddafi
Hoto: ADEM ALTAN/AFP/Getty Images

Tare da karsashi, kakakin majalisar rikon kwarya na wancan lokaci Abdel Hafez Ghoga a ranar 20 ga watan Oktoba 2011, ya sanar da mutuwar Muammar Gaddafi yana cewa muna sanar da duniya Gaddafi ya mutu a hannun 'yan gwagwarmayar juyin juya hali. Wannan ya kawo karshen zalunci da mulkin danniya a Libya.

'Yan watanni kafin wannan lokaci, a watan Fabrairun 2011 'yan Libya suka yi koyi da boren juyin juya hali a makwabciyarsu kasar Tunisiya suka bijire wa shugaban kasar Muammar Gaddafi wanda ya hau karagr mulki tun 1969 bayan juyin mulkin soji.

Ban Ki-moon The Global Commission on Adaptation
Ban Ki Moon, tsohon Sakataren MDDHoto: Getty Images/AFP/G. Baker

A watan Maris, Majalisar Dinkin Duniya ta ba da sahalewar afka wa Gaddafi da karfin soji da manufar kare musamman jama'a fararen hula. Farmakin da kungiyar kawancen tsaro ta NATO ta kai kan cibiyoyin rundunar sojin Gaddafi ya taimaka wajen kassara shi da kuma karya lagon shugaban.

Bayan tsawon watanni yana buya, a karshe ya fake a birnin Sirte a arewacin kasar, tazarar kilomita 450 daga gabashin Tripoli. Sakamakon kawanya da yan adawa suka yi masa shugaban ya nemi tserewa ta wata katuwar rariya amma sai aka kama shi. Nan take 'yan adawar suka far masa tare da yi masa kisan gilla.

 

A wasu lokutan an yi dokin cewa za a sami sabuwar rayuwa a Libya inda jama'a suka cika da fata mai yawa. Sai dai ko a wancan lokacin an yi ta gargadi da jan hankali kamar yadda Sakataren Majalisar Dinkin Duniya na wancan lokaci Ban Ki Moon ya yi.

Ya ce "za mu ga yanayi na murna da kuma bakin ciki ga wadanda suka yi rashi mai yawa. Amma duk da haka ya kamata mu gaggauta sanin cewa wannan karshe ne kuma mafari ga abin da zai zo a gaba. Kalubalen da ke gaban Libiya da al'umarta yana da yawa. Yanzu lokaci ne da 'yan Libya za su hada kansu su sasanta da juna. Mayaka na kowane bangare su ajiye makamansu su rungumi zaman lafiya. Wannan lokaci ne na gina kasa da yafe wa juna, ba na ramuwar gayya ba."

Libyen Bürgerkrieg
Wasu makaman da ake amfani da su a LibiyaHoto: picture-alliance/dpa/EPA/M. Messara

Rashin gamsuwar da galibin al'ummar Libya suka nuna da mulkin Gaddafi, ya samo asali ne daga dalilai na tattalin arziki da walwala kamar tashin farashin kayan abinci da kuma tsananin rashin aiki ga matasa a cewar Hager Ali mai bincike a cibiyar GIGA dake birnin Hamburg mai nazari kan al'amuran Gabas Ta Tsakiya.

A sakamakon matsalolin da Libiya ta fada ciki kasar ta nemi wargajewa aka sami gwamnatoci biyu, daya a Tripoli babban birnin kasar dayan kuma a birnin Tobruk mai tashar jiragen ruwa a gabashin kasar.

Har yanzu dai matsaloli da dama na Libya ba a warware su ba, ga kalubalen yaduwar makamai sannan ga rashin tabbas na wanzuwar dimukuradiyya kuma an kasa shawo kan mayakan sa kai wadnda basa bin umarni ballantana sanin doka da oda.