1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru 20 da rushewar katangar Berlin

Umaru AliyuOctober 23, 2009

Eric Singh ya shaidar da rushewar katangar Berlin

https://p.dw.com/p/KDh6
Murnar rushewar katangar Berlin

Neman tuna yadda rayuwa ta kasance a yankin Jamus ta gabas, al'amari ne da kan kasance mai matukar sarkakiya ga su kansu mazauna wannan yanki. Suma baki yan ci rani da suka taba zama a yankin na Jamus ta gabas, basa samun saukin bayanin irin halin da suka zauna karkashin sa a yankin. Daya daga cikin irin wadannan baki da suka zauna a Jamus ta gabas din har zuwa ranar tara ga watan Nuwamna na shekara ta 1989, shine Eric Singh. Haifaffen Afrika ta kudu, Singh ya tsere ne zuwa Jamus ta gabas daga Durban, domin ya kauracewa gallazawa a kasar sa.

Daga Berlin ta gabas, dan gwagwarmayar na kungiyar ANC yaci gaba da nuna adawar sa ga mulkin wariya, inda har ma ya rika samun goyon baya da taimakon kudi daga hukumomin wannan yanki. Har ma bayan rushewar katangar ta Berlin, Eric Singh yaci gaba da zama a Berlin, inda a yanzu yake tuna rayuwa a Jamus ta gabas da rushewar katangar Berlin.

Shin ana iya cewar wannan hira da manema labarai ya canza al'amuran duniya. Wannan dai tabbas haka yake, a bisa ra'ayin yan jarida da suka hallara, suka saurari jawabin Günter Schabowski, kakakin gwmanatin kwaminisanci ta Jamus ta gabas, ranar tara ga watan Nuwamba na shekara ta 1989 a Berlin ta gabas. A wannan rana, Schabowski ya sanar da matakan sassauta tafiye-tafiye zuwa ketare ga yan Jamus ta gabas. Eric Singh ya halarci wannan taro na manema labarai, saboda daga can Berlin ta gabas ya rika aikawa mujallu dabam dabam sharhuna da rahotanni. Saboda haka ma Singh yace yayi imanin ya kasance cikin wadanda suka shaidar da wani al'amari na tarihi. Yace:

"Na bi wannan taro na yan jarida a tsanaki, kuma naji tambayar da Ricardo Ehrmann daga Italiya yayi, inda ya tambayi shin wane lokaci ne za'a bude iyakokin na Jamus ta gabas? Shi kuma Schabowski ya amsa da cewa yau".

Jim kadan kuwa bayan wannan hira da yan jaridu, wanda ma gidan television na hukuma ya nuna kai tsaye, aka fara samun yan Jamus ta gabas da suka yi kasadar zuwa kan iyakokin da suka raba tsakanin Berlin ta gabas da Berlin ta yamma. Masu tsaron kan iyakokin, wadanda ma tururuwar jama'a ta nemi fin karfin su, suka kyale jama'a su tsallaka zuwa daya bangaren, wanda har ya zuwa wannan lokaci aka haramtawa yan Jamus ta gabas shi. Nan da nan kuwa labarin haka ya watsu ko ina, inda jama'a suka rika cunkoso a wuraren kan iyaka a Berlin ta gabas, domin neman tsallkawa zuwa yamma da kuma samun yancin su. Ya zuwa tsadar dare aka bude dukkanin iyakokin, katangar Berlin ta zama sai labari. Shi kansa Eric Singh ya shaidar da wannan babban abu na tarihi ne a washegari, inda ya shiga jirgin kasa daga tashar Friedrichstrasse a Berlin ta gabas zuwa yankin Berlin ta yamma. Yace:

"Daga Friedrichstrasse na isa kan iyaka, inda na taras da dubban jama'a, musmaman matasa. Daga nan muka tsallaka kogin Spree zuwa Berlin ta yamma. Na kuma fahimci yadda dimbin jama'a sukai ta nuna bukatar su ta zuwa ga samun yanci, saboda ni kaina na kasa samun damar tserewa daga Afrika ta kudu lokacin da naso, saboda a matsayi na na dan gwagwarmaya adawa da wariya, bani da yancin fita zuwa ketare, saboda bani da paspo".

A yau, Eric Singh yana nuna matukar godiyar sa ga dukkanin taimako da goyon bayan da ya samu daga Jamus ta gabas kasar da a bana, shekaru ashirin kenan da bacewar ta. Yace duk da mummunan kasawar yankin a bangaren democradiya da kuma matakai masu tsanani kan yan adawa, amma Jamus ta gabas ta bada gudumuwa mai yawa a gwagwarmaya kan gwamnatin wariya ta Afrika ta kudu. Yace:

"A nan ko da shike mutane basu da yancin tafiye-tafiye yadda suka so, amma sun karbi wannan hali cikin kwanciyar hankali. Na kan tattauna haka din da matata ta, wdada ita ma yar Jamus ta gabas ce. Takan ce a da can nayi rayuwa ce ba tare da hatsaniya ba, amma ba haka abin yake ba a yanzu. Bayan da aka rushewa kasar, ta rasa aikin ta a matsayin mai fassara saboda wai ta tsufa. Ba kuwa ita kadai ba, jama'a da dama sun shiga irin wannan hali.

Yanzu Eric Singh yana zaune cikin farin ciki da jin dadi da matar sa a Berlin. Dan jaridar da yayi ritaya har yanzu yana da alaka ta kurkusa tare da Afrika ta kudu, kasar da tun bayan kawo karshen mulkin wariya yake mallakar paspo din ta.

Mawallafi: Umaru Aliyu

Edita: Tijani Lawal