1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru 25 da hadewar Jamus ta Yamma da ta Gabas

Muhammad Nasiru Awal / LMJOctober 2, 2015

A wannan Asabar din uku ga watan Oktoba aka cika shekaru 25 da sake hadewar kasashen Jamus ta Yamma da Jamus ta Gabas inda yanzu haka hadaddiyar kasar ke taka rawar gani tsakanin kasashen Turai.

https://p.dw.com/p/1GhwI
Dan-dazon mutane a yayin da aka kayar da bangon Berlin da ya raba Jamus ta Gabas da ta Yamma
Dan-dazon mutane a yayin da aka kayar da bangon Berlin da ya raba Jamus ta Gabas da ta YammaHoto: picture-alliance/dpa

Tun bayan sake hadewar kasashen biyu a ranar uku ga watan Oktoba na shekarar 1990, hadaddiyar kasar ta Jamus ta taka rawar jagoranci iri daban-daban a nahiyar Turai, abin da kuma ke canjawa koda yaushe. Shin ko Jamus din ta zama wata daula mai sara tana duban bakin gatari ko kuma ta zama mai kwadayin mulki ne? Ra'ayoyi dai sun banbanta game da rawar da Jamus ke takawa tsakanin kasashen Turai tun bayan sake hadewarta shekaru 25 din da suka gabata. Yayin da wasu masharhanta ke da ra'ayin cewa Jamus din tana jagorancin Turai ba tare da ta sani ba, wasu kuwa zargin ta suke da kokarin mamaye al'amura a nahiyar ta Turai. Duk da haka dai ra'ayi ya zo daya cewa a wannan lokacin shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ce wata shugaba mai kishin nahiyar Turai wadda ke sara tana duban bakin gatari kana tana la'akari da kasar Faransa.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel
Shugabar gwamnatin Jamus Angela MerkelHoto: picture-alliance/dpa/J. Woitas

Hada kai da jagoranci

Bisa al'ada dai kasashen Faransa da Jamus ne kashin bayan hadin kan Turai da ke kuma jan akalar duk wani ci-gaba a nahiyar, inji Elmar Brok na kwamitin kula da harkokin kasashen ketare na majalisar Turai wanda kuma dan majalisar Turai ne lokacin hadewar kasashen Jamus.

Ya ce: "A gani na Jamus ba ta son yin jagorancin ita kadai. Saboda haka muke fata Faransa za ta shigo a dama da ita 100 bisa 100. Sai dai ina ganin dole sai tattalin arzikin Faransa ya kara ingantuwa sannan ne ita da Jamus za su iya taka rawa ta jagoranci su biyu."

Elmar Brok ya kara da cewa wani muhimmin abu kuma shi ne shigar da kasar Poland cikin jagororin na Turai. A halin nan da ake ciki na rikicin kudin Euro da tabarbarewar tattalin arzikin kasar Girka da kuma matsalar 'yan gudun hijira, sau tari Jamus ce ke da fada a ji. Sai dai kuma manufofinta kan tsimin kudi ya sa Jamus tana rarraba kan Turai. Saboda haka ya kamata Jamus ta yi takatsantsan ka da ta janyo wa kanta bakin suna daga kananan kasashe na Turai inji Elmar Brok.

Shugaban gwamnatin Jmasu na farko Konrad Adenauer
Shugaban gwamnatin Jamus na farko Konrad AdenauerHoto: picture-alliance/dpa

Jamus ka iya ci gaba da taka rawa a Turai

Guy Verhofstadt da ke zama tsohon Firaministan kasar Beljiyam ya ce Jamus ka iya ci gaba da taka muhimmiyar rawar gani a Turai.

Ya ce: "Mun rasa wani matsayi tun bayan sake hadewar Jamus, kuma ta karbi jan ragamar samun cikakken hadin kan nahiyar Turai. Wannan kuwa ya kasance babban aiki na tarihi da Jamus ta yi cikin karni na 20 da ya gabata. Ina fata Jamus za ta ci gaba da wannan jagoranci. Muna bukatar jagorancinta."

Sai dai masanin harkokin ketare na Tarayyar Turai Elmar Brok ya ce nakasu a rawar da Jamus ke takawa a nahiyar Turai shi ne yadda ita da kasar Faransa ke tafiyar da huldodin ketare na bai-daya. Ko shakka babu akwai kyakkyawan hadin kai tsakanin Jamus da Faransa sai da abin da ake rshin sa shi ne fuskantar alkibla ta bai-daya dangane da makomar nahiyar Turai.