1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru 30 bayan rasuwar Seyni Kountche

Mahaman Kanta
November 10, 2017

A wannan Juma'ar (10.11.2017) ce tsohon shugaban mulkin sojan Nijar Seyni Koutche ya cika shekaru goma da rasuwa, wannan ne ma ya sanya aka ware wasu kwanaki domin bukukuwan tunawa da shi.

https://p.dw.com/p/2nQky
Niger Flagge
Al'ummar Nijar sun gudanar da addu'o'i ga tsohon shugaban kasar Seyni Kountché wanda ya rasu shekaru 30 da suka gabata

Tun ranar talatar da ta gabata ce aka fara makon tunawa da shi inda aka shirya wani taro a zauren taruka na kasa wato  da ke birnin  Yamai. A wannan waje an gwada hotunansa da kuma majigin nuna ayyukkan da yai tsowon shekaru 13 da ya shafe ya na mulkar Jamhuriyar ta Nijar. Baya ga wannan, tsofaffin mukarraban gwamnatin ta Kountche ciki har da Dakta Mahaman Oumaru wanda shi ne firaminista a lokacin mulkin na Kountche sun gudanar da jawabai inda suka ce mutum ne dan kishin kasa.

Niger Kongresszentrum in Niamey
An gudanar da taro inda aka yi ta jawabai kan irin aiyyukan da tsohon shugaban Nihar Seyni Kountché ya yi a lokacin mulkinsaHoto: DW/M. Kanta

Shi kuwa Alhaji Ila Maikasuwa wanda ya jagoranci ma'aikatar Ilimi da tarbiyya a zamanin na Kountche ya ce tsohon shugaban ya yi bakin kokarinsa wajen ganin ya bunkasa ilimi a kasar domin kuwa an saka malamai cikin yanayi mai kyau sannan ana biyan malamai hakkinsu a kan lokaci kana dalibai sun samu dama ta yin karatu a yanayi mai kyau.

Duk da cewar ya samu nasarori a lokacin mulkin nasa, kasar ta Nijar ta fuskanci matsaloli ciki kuwa har da karancin kudi da fari wanda ya haifar da karancin abinci da kuma mutuwar dabbobi to amma shugaban ya yi kokari wajen warware wadannan matsaloli inda a wannan lokaci ya bukaci yin aiki tare da Dakta Boukari Aji wanda aka nada a matsayin ministan kudi. A wannan lokacin sun dau matakai na karbar wani kaso daga wajen ma'aikata musamman ma manyan jami'an gwamnati don yin amfani da kudin wajen gina kasa wadda hakan ya taimaka wajen samun sauki kalubalen da aka shiga.