1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru 70 da kafa kotun hukunta masu laifukan yaki a Jamus

September 30, 2016

Ranar daya ga watan Oktoba aka cika shekaru 70 da gudanar da shari'ar tsofin jami'an gwamnatin 'yan Nazi a nan Jamus, wadanda aka tuhuma da laifukan yaki lokacin yakin duniya na biyu.

https://p.dw.com/p/2QmBe
Nürnberger Kriegsverbrecher Prozess
Hoto: AP

Ranar daya ga watan Oktoba shekara ta 1946 aka kammala shari'ar da aka gudanar da ita a binin Nuremberg, inda 22 daga cikin wadanda aka yi wa shari'ar aka yanke masu hukuncin kisa ta hanyar rataya, wasu bakwai aka yanke masu hukuncin zaman gidan kaso a kurkukun Spandau, wasu mutanen uku kuma ba a same su da laifi ba.

Hukuncin da kotun ya zartas a karshen shari'ar ta Nuremberg, ta kawo karshen tuhumar da aka yi wa mutane 2630, inda kuma aka saurari shaidu kimanin 270. Shari'ar dai ta zama ta farko a duniya, inda wata kotun soja na kasa da kasa ta zartas da hukunci ta hanyar shari'a. Kafin wannan lokaci, ba a taba samun inda masu mulkin kama karya suka ga gaskiyar cewar ana iya yanke wani hukunci saboda wani laifi da suka aikata ba, amma a wannan karo, mataimakan Hitler sun fuskanci shari'a, aka kuma yanke masu hukunci da sunan al'ummar duniya baki daya a birnin na Nuremberg. Tun kafin a fara shari'ar sai da manyan daulolin duniya da suka cinye Jamus da yaki suka tsara tafiyar da shari'ar da kuma hukuncin da ya dace a zartas kan wadanda ake tuhuma idan har aka same su da laifi, bayan sun sanya hannu ranar takwas ga watan Agusta na shekara ta 1945, kan yarjejeniyar London game da tsarin wannan shari'a.

Nürnberger Kriegsverbrecher Prozess Hermann Göring
Hoto: AP

Amirka dai  ita ce ta fara kawo shawarar  gurfanar da mukarraban na mulkin Nazi gaban shari'a, saboda tun a lokacin yakin duniya na biyu Amirkawa suka fara tara bayanai na sirri a game da manyan laifukan na  Jamusawan da abokan hadin gwiwarsu suka rika aikatawa. Robert Kemper, daya daga cikin wadanda suka gabatar da 'yan Nazin gaban shari'a  ya ce tun kafin a fara shari'ar ya tambayi kansa ko za a taba samun bayanan da za su zama shaida na irin rashin imani da 'yan Nazin suka aikata.

Shari'ar dai an fara ba tare da an san yadda za ta kare ba. Herman Göring, babban hafsan hafsoshin rundunar jiragen saman Hitler da ya bayyana gaban shari'ar ya shaida wa kotun cewar babu wani abin da ya masu neman yi masa shari'a da abin da ke gudana.

Tsohon firaminista ministan, Winston Churchill na Birtaniya ya bayyana shakkunsa a game da dacewar shari'ar ta Nuremberg. A bisa ra'ayinsa, duk wadanda aka zarge su da aikata laifi a zamanin Hitler kamata ya yi a harbe su kawai ba tare da shari'a ba. 

Nürnberger Prozess 1946
Hoto: picture alliance/ZB

Duk wadanda ake tuhuma, sun rika fake da Adolf Hitler, tare da nuna cewar abubuwan da suka aikata sun yi ne bisa amsa umurni daga gare shi, kamar yadda Johann Schäzler mataimakin lauyan da ya kare mukaddashin Hitler, Rudolf Hess ya nunar.

Ranar daya ga watan Oktoba shekara ta 1946, alkali Geoffrey Lawrence daga Birtaniya ya rufe shari'a bayan ya karanto hukuncin da aka yanke wa wadanda aka zarge su da aikata laifukan a zamanin mulkin Nazi.