1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru biyar da juyin juya hali a Masar

Jürgen Stryjak/ ZMA January 25, 2016

Dandalin Tahrir da ke birnin Alkahira ya kasance alamar boren da ya kifar da mulkin kama karya na tsawon shekaru a Masar.

https://p.dw.com/p/1HjfJ
Ägypten Menschen feiern den 5. Jahrestag der Revolution am Tahrir-Platz
Hoto: Reuters/M. Abd El Ghany

A wannan Litinin din ce Masar ta cika shekaru biyar da gudanar da zanga-zangar juyin juya hali a dandalin taro na Tahrir da ke birnin Alkahira, a wani mataki na neman 'yancin al'umma. Dubban daruruwan Misirawa ne dai suka shiga wannan gangami da ya jagoranci kifar da gwamnatin shugaban kama karya Hosni Mubarak.

Shekarun Karim Farid 19 a ranar 25 ga watan Janairun shekara ta 2011, ranar da aka kaddamar da wannan gangami. Midan at-Tahrir dai na nufin "Dandalin 'Yanci", kuma Farid ya kasance daya daga cikin dubban daruruwan Misirawa da suka yi jerin gwano zuwa dandalin na Tahrir domin kaddamar da juyin juya halin.

"Tun daga ranar farko na kasance a wurin. Sadaukarwa ce. Ina da idanu guda biyu wadanda ke ganin halin takaici da kasata ke ciki. Abun da ke raina a matsayin matashi shi ne, kyakkyawan fata."

Kokarin tarwatsa masu zaman dirshan ya ci tura

Da daddare jami'an tsaro sun cimma nasarar korar mutane da hayaki mai sa hawaye da kame kame.

"Irin yadda na ji a wannan lokaci a dandalin na Tahrir ya yi tasiri wajen sauya rayuwata. Na hadu da Misirawa masu sassaucin ra'ayi da 'yan ra'ayin rikau da masu kishin Islama. Wadanda duk ke fafutukar abu guda wato 'yanci da adalci. Nan take na san akwai kyakkyawan fata."

Ägypten Sicherheitsmaßnahmen am 5. Jahrestag der Revolution
An tsaurara matakan tsaro a ranar cika shekaru biyar da juyin juya haliHoto: Reuters/M. Abd El Ghany

Yini uku bayan tarwatsa gangamin, dubban mutane suka sake bazama kan tituna a wata sabuwar zanga-zangar cimma buri har sai da Shugaba Hosni Mubarak ya yi murabus.

"Isqat an-nizam": Babu wakar da ta fi wannan daukar hankali a lokacin juyin juya halin, wanda ke nufin "Al'umma na muradin rushewar wannan gwamnati". A ranar 2 ga watan Fabrairu jami'an tsaro sun sake yunkuri na karshe wajen ruguza wannan gangami. Sun aike da tawagar 'yan banga a kan rakuma da dawakai zuwa dandalin na Tahrir, domin tarwatsa masu zanga-zangar.

Sai dai masu gangamin sun cimma nasarar kare wannan dandali, wurin da ya zame musu dandalin fafutukar neman 'yanci.

Dandalin fafutukar neman 'yanci

Kade-kade da wake-waken neman 'yancin sun ci gaba da daukar hankalin wadanda ke da alaka da neman 'yanci. Kazalika ana barin duk wanda ke muradin yin jawabi ya yi. A garesu wannan buki ne na samun 'yanci. A ranar 11 ga watan Fabrairu shugaba Hosni Mubarak ya yi murabus daga kujerar mulki.

Burin Karin Farid a rayuwa shi ne ya zama dan jarida. Shekaru bayan wannan fitaccen juyin juya hali, a yanzu haka yana aiki a matsayin mai dauko rahoto ga wani fitaccen gidan talabijin a kasar.

Ägypten Tahrir-Platz am 5. Jahrestag der Revolution
Dandalin Tahrir shekaru biyar bayan boren neman 'yanciHoto: Reuters/M. Abd El Ghany

Daga baya dandalin na Tahrir ya zame wani wuri na rikici tsakanin mabiya darikun kasar. Dandalin a baya ya kasance tamkar gidan kowa. Yau idan masu sassaucin ra'ayi suka yi taro, gobe masu ra'ayin mazan jiya. A wasu ranaikun ma dubban daruruwan masu tsananin kishin addinin Islama ne ke gangami.

Sojojin kasar sun ci gajiyar wannan sabani da tashe tashen hankulan, inda suka cimma nasarar kifar da zababbiyar gwamnati a shekara ta 2013. Dandalin 'yanci na Tahrir ya sake komawa karkashin ikonsu.

"Gwamnati na yaki da 'yancin walwala da tofa albarkacin baki, tare da barazana ga mutane. Hakan ya sa muna tsoro dangane 'yanci da ma demokradiyya. Kamata ya yi ac e muna kaunar 'yan sanda saboda su ya kamata ac e suna kare mu. Amma wannan gwamnati na cin zarafinmu, ta take hakkokinmu tare da hana mu 'yancinmu na walwala."

Shirin da Karim Farid ke gabatarwa a gidan talabijin dai na cikin garari. Don haka ne ma matashin dan jaridar mai hazaka yake shirin barin kasarsa ta haihuwa. Ya na muradin neman sabon aiki a birnin Dubai, na Hadaddiyar Daular Larabawa.